ECOWAS Ta Fara Aikin Jigilar Motocin Ambulans Na Yankin A Togo

ECOWAS ta hannun Hukumar Kula da Lafiya ta Yammacin Afirka (WAHO) tare da haɗin gwiwar Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da Ayyukan Aiwatar da Shirye-shirye (UNOPS) sun shirya bikin mika motocin daukar marasa lafiya (ambulances) guda 30 kirar Land Cruiser 78 Series wadanda aka sanye su da kayan aikin likitanci na zamani domin amfanin kasashen da ke cikin kungiyar ECOWAS.
An gudanar da bikin ne a birnin Lomé na kasar Togo inda Shugaban Hukumar ECOWAS Dr. Omar Alieu Touray da Mataimakiyar Shugaban Hukumar ECOWAS Ms. Damtien Tchintchibidja suka halarta tare da Ministan Lafiya da Tsabtace Muhalli da Shirin Samar da Inshorar Lafiya ga Kowa na kasar Togo Mr. Jean-Marie Tessi da Darakta Janar na WAHO Dr. Melchior Athanase Aïssi da Mr. Kossi Edjam wakilin Kungiyar Red Cross da Red Crescent ta Duniya da kuma wakilan kasashen da ke cikin ECOWAS.
Bikin ya kuma yi nuni da fara aikin rarraba wadannan motoci zuwa kasashen da za su amfana da su a hukumance.
KARANTA KUMA: ECOWAS da AU Sun Daidaita Tsarin Matasa na Samar da Zaman Lafiya
A cikin jawabinsa da farko Dr. Touray ya bayyana matukar godiyarsa ga Shugaban Majalisar Ministocin kasar Togo Mr. Faure Gnassingbe da kuma gwamnati da al’ummar kasar Togo bisa karramawar da suka yi musu.
Ya bayyana cewa samar da wadannan motoci 30 ba wai kawai yana nuna kudurin ECOWAS da WAHO da UNOPS da kasashen mambobi ne na karfafa tsarin kiwon lafiya inganta samun kulawar gaggawa, da kuma ci gaba da manufar samar da inshorar lafiya ga kowa ba har ila yau sakamako ne na kyakkyawan hadin gwiwa a yankin wanda ya ginu kan hadin kai da juriya da kuma daukar nauyi tare tare da sanya jin dadin al’umma a matsayin babban abin da aka fi mayar da hankali a kai.
“Ta hanyar wannan shiri muna sake tabbatar da cewa ECOWAS kungiya ce mai daukar mataki kungiya mai kare al’umma da kuma kungiya mai sanya jin dadin dan adam a gaba a cikin tsarin hadin kan kasashen yankin” in ji shi.
Mataimakiyar Shugabar Hukumar Ms. Tchintchibidja ta bayyana cewa tana jin motsin rai da kuma gamsuwa da cimma nasara yayin da take halartar wannan taron wanda ke daya daga cikin ayyukan hukuma na karshe na hukumar mai barin gado bayan wa’adin shekaru hudu da aka fuskanci manyan kalubale a fannin kiwon lafiya da tsaro da kuma tsarin hukumomi.
Ta kuma yaba wa Shugaban Hukumar ECOWAS Dr. Omar Alieu Touray bisa jagorancinsa tare da taya kwamishinoni Darakta Janar na WAHO ma’aikatan hukumomin kasashe mambobi da kuma UNOPS murna bisa kwazon da suka nuna yayin da ta yi kira da a ci gaba da manufar kungiyar.
“Hukuma na zuwa ta tafi amma manufa na ci gaba da wanzuwa. Hukumomin kungiyarmu sun fi karfin mutanen da ke yi musu aiki na wani lokaci girma. Shi ya sa nake fatan ayyukan da muka fara za su ci gaba da irin wannan kuduri kuma ina ba da karfin gwiwa ga wadanda za su samu damar karbar ragamar aikin daga hannunmu.
Wadannan motocin daukar marasa lafiya guda talatin za su ci gaba da kasancewa dogon lokaci bayan mun tafi a matsayin shaida ta zahiri kan abin da muka yi kokarin cimma tare: kusantar da ayyukan kiwon lafiya ga al’ummomi karfafa karfin yankinmu wajen tunkarar matsalolin kiwon lafiya da kuma sanya hadin kai da dunkulewar yankin a fannin kiwon lafiya su zama abin da ake gani a aikace kullum ga al’ummar Yammacin Afirka” in ji ta.
Ministan Lafiya da Tsabtar Muhalli na Togo Mr. Tessi ya yaba wa ECOWAS da WAHO a madadin gwamnatin Togo bisa wannan shiri wanda ke taimakawa wajen inganta da karfafa karfin tsarin kiwon lafiya a Togo da sauran kasashen da ke mambobi a ECOWAS.
A jawabinsa Dr. Aïssi ya jaddada cewa an samu nasarar aiwatar da wannan shiri ne sakamakon jagorancin Hukumar ECOWAS hadin gwiwa mai muhimmanci tsakanin WAHO da UNOPS da kuma goyon bayan kasashe mambobi.
Ladan Nasidi



