NajeriyaSiyasa

JAM’IYAR ACCORD TA LASHE ZAƁEN GWAMNAN A JIHAR OSUN

Kabiru Yusuf ,Osun

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta sanar da gwamna mai ci Ademola Adeleke na jam’iyyar Accord a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar ranar Asabar 15 ga watan Agustan 2026.

Adeleke ya fafata ne a zaben da sauran ‘yan takara 15  ciki har da dan takarar jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya Bola Oyebamiji wanda shi ne fafatawar ta fi zafi a tsakaninsu baya ga sauran jam’iyun da suka shiga takarar

Babban jami’in zabe na hukumar Zaɓe Mai zaman kanta ta Najeriya INEC a zaɓen wanda ya sanar da sakamakon da sanyin safiyar ranar Lahadi Farfesa Oluwatoyin Ogundipe ya bayyana cewa Adeleke ya samu jimillar kuri’u 511,067 yayin da Oyebamiji na jam’iyyar APC wanda ya zo a matsayi na biyu ya samu jimillar kuri’u 444,815.

Zuwa yanzu dai babu wani labari na tashin hankali sai dai ko ina ka za ga a birnin Oshogbo magoya bayan jam’iyar ACCORD ke sowa bisa nasarar da jam’iyar tasu ta samu a wannan zaɓe wanda shi ake yi masa kallon zakaran gwajin dafi.

Ƙungiyoyi masu sa ido a zaɓen gwamnan jihar Osun sun bayyana cewa zaɓen ya gudana cikin kwanciyar hankali da oda kodayake sun bayyana damuwa kan matsalolin na’urorin BVAS a wasu wuraren da sauran wasu matsalolin da ba a rasa ba.

 

 

Kabiru Yusuf

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button