Ademola Adeleke Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Osun

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ayyana Gwamnan Jihar Osun mai ci Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna na shekarar 2026.
Adeleke wanda shi ne dan takarar jam’iyyar Accord Party ya samu kuri’u 511,067 inda ya doke babban abokin hamayyarsa Bola Oyebamiji na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wanda ya samu kuri’u 444,815
Jami’in INEC mai kula da zaben Farfesa Joshua Olalekan Ogunwole ne ya sanar da sakamakon a ranar Lahadi bayan kammala tattara sakamakon zaben daga dukkan kananan hukumomi 30 na jihar.
Ta hakan dan takarar jam’iyyar Accord Party ya samu damar yin wa’adi na biyu a matsayin Gwamnan Jihar Osun.
Dan takarar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) Najeem Salaam ya zo na uku da kuri’u 17,180.
An yi wannan sanarwar ne bayan kammala kada kuri’u da tattara sakamakon zaben daga kananan hukumomi 30 na jihar.
An gudanar da zaben wanda ya ja hankalin masu kada kuri’a a fadin jihar a rumfunan zabe 3,763 da ke warwatse a yankunan rajistar zabe 332.
Bisa wannan sanarwar Adeleke zai ci gaba da rike mukamin Gwamnan Jihar Osun na tsawon wani wa’adin shekaru hudu.
LADAN NASIDI



