Najeriya

Kiristocin Katolika Barno Suna Addu’ar Samun Zaman Lafiya Mai Dorewa

Addu’o’in neman zaman lafiya mai dorewa a Jihar Borno da kuma kawo karshen ta’addanci da tashin hankali ne suka mamaye bikin Ranar Daukakar Budurwa Maryamu (Assumption of the Blessed Virgin Mary) a Babban Cocin St. Patrick da ke Maiduguri.

Mabiya addinin Katolika daga sassa daban-daban na birnin sun taru a babban cocin domin gudanar da bikin inda suka yi addu’ar samun zaman lafiya da hadin kai da tsaro a Jihar Barno da ma Najeriya baki daya.

Bikin ya kuma ba mabiya addinin damar nuna godiya kan yanayin zaman lafiyar da ake samu a wasu sassan jihar bayan shekaru na rashin tsaro tare da ci gaba da yin addu’o’in ganin an dawo da cikakken zaman lafiya a dukkan al’ummomin da rikicin ‘yan ta’adda ya shafa.

Ga yawancin masu ibadar taron ya kasance lokaci ne na bege karfin gwiwa da kuma godiya. Wasu sun ba da labarin yadda suka jure shekaru na tashin hankali da wahalhalu tare da ci gaba da tsayawa tsayin daka kan imaninsu.

Bishop na Cocin Katolika na Maiduguri Most Reverend Oliver Dashe Doeme wanda ya gabatar da jawabi tare da jagorantar addu’o’i a yayin bikin ya bukaci muminai da su ci gaba da himmantuwa wajen yin addu’a a matsayin hanyar samun nasara kan ta’addanci da kuma tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

Da yake tsokaci kan hare-haren baya-bayan nan a wasu yankuna na jihar Barno Bishop Dashe ya bayyana cewa dole ne a rika tafiyar da addu’a tare da daukar matakai masu karfi daga bangaren hukumomi.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Borno da su dauki dukkan matakan da suka dace domin karfafa ayyukan tsaro tare da tabbatar da cewa jami’an tsaro suna da kayan aiki da damar shiga dazuzzuka da yankuna masu tsaunuka inda ake zargin ‘yan ta’adda na gudanar da ayyukansu.

“Muna addu’ar a murkushe Boko Haram, amma dole ne mutane ma su yi nasu bangaren na aiki” in ji Bishop Dashe yayin da yake kira ga hukumomi da su dauki matakan da suka dace domin kawar da ‘yan ta’adda da kuma dawo da zaman lafiya a jihar Borno da ma Najeriya baki daya.

Bishop Dashe ya kuma yi kira ga Kiristoci da su kasance masu taka-tsantsan inda ya jaddada cewa addu’a na daya daga cikin muhimman hanyoyin da masu imani za su bi wajen tunkarar halin da ake ciki na tsaro.

Ya bayyana cewa masu imani sun taru ne domin yin addu’a da gode wa Budurwa Maryamu da kuma neman dorewar zaman lafiya a rayuwarsu, da majami’unsu da kuma al’ummominsu.

“Bari addu’a ta zama abu mafi muhimmanci a rayuwarmu a matsayinmu na masu imani. Idan muka nutsu cikin addu’a Allah zai ba mu nasara” in ji shi.

Bishop din ya yaba wa Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum bisa goyon bayan da gwamnatinsa ke bai wa jami’an tsaro da kuma ayyukan jin kai da take gudanarwa domin tallafa wa al’ummomin da rikicin ya shafa.

Ya jaddada bukatar ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, hukumomin tsaro cibiyoyin addini da al’ummomin yankin don ƙarfafa zaman lafiyar da ake fuskanta a sassan jihar.

Bishop Dashe ya bukaci mutane da su ci gaba da kasancewa masu bege da kuma jajircewa wajen samar da zaman lafiya da afuwa da sulhu yayin da yake addu’ar kawo ƙarshen tashin hankali da kuma dawo da rayuwa ta yau da kullun a cikin dukkan al’ummomin da rashin tsaro ya shafa.

Taron tunawa da cika shekaru 100 na Haihuwar Annabi Isa (AS) ya kasance ba kawai a matsayin babban biki na addini ba har ma a matsayin dandamali na godiya tunani da kuma sabunta alƙawarin zaman lafiya da tsaro a Jihar Borno.

 

LADAN NASIDI

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button