Shugaba Tinubu Ya Yi Kira Da A Gudanar Da Zaben Wamnan Jihar Osun Cikin Lumana Da Kuma Sahihanci

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira da a gudanar da zaben gwamna cikin kwanciyar hankali da ‘yanci da adalci a Jihar Osun inda ya umurci hukumomin tsaro su tabbatar da kare masu kada kuri’a yayin da ake shirin gudanar da zaben a ranar 15 ga watan Agusta 2026.
Har ila yau Shugaba Tinubu ya kalubalanci hukumar zabe da ta yi amfani da zaben gwamnan na Osun wajen nuna shirye-shiryenta na gudanar da babban zaben shekarar 2027.
“Dole ne INEC ta yi amfani da wannan zabe na musamman (wanda ba ya zuwa lokaci guda da sauran zabuka) a matsayin gwaji don nuna wa ‘yan Najeriya cewa ta shirya tsaf domin zaben 2027” in ji shi.
Dangane da batun tsaro Shugaban ya bayyana cewa ya umurci Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda da shugabannin sauran hukumomin tsaro da ke da hannu a zaben su samar da isasshen tsaro a rumfunan zabe tare da dakile duk wani yunkuri na kawo cikas ga tsarin zaben.
KARANTA KUMA: INEC ta yi alkawarin gudanar da ingantaccen zaben gwamna a Osun
“Na umurci Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda da sauran shugabannin hukumomin tsaro da ke shiga cikin zaben su samar da cikakken tsaro a rumfunan zabe. Bai kamata a ba masu son haifar da rikici damar kawo cikas ga tsarin zaben ba”
“Yayin da al’ummar Jihar Osun ke shirin zuwa rumfunan zabe domin zaben wanda zai shugabance su na tsawon shekaru hudu masu zuwa ina kira ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta tabbatar an gudanar da zaben cikin tsari. Dole ne zaben ya kasance mai nuna gaskiya da ‘yanci da adalci. Ina karfafa gwiwar INEC wajen tabbatar da amincin tsarin zaben” in ji Shugaban kasa yana mai jaddada hakan.
Haka kuma Shugaban na Najeriya ya yi kira ga masu zabe da su fito kwansu da kwarkwatarsu su sauke nauyin da ya rataya a kansu na zabe cikin lumana tare da guje wa duk wani mataki da ka iya kawo cikas ga zaben.
“Ya kamata masu zabe su kasance da kwarin gwiwar fitowa da yawa domin zaben dan takarar da suka zaba kasancewar an samar da dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da zabe mai cike da lumana da ‘yanci da adalci” in ji shi.
Ya kuma bukaci INEC da ta tabbatar an gudanar da tsari mai nuna gaskiya da tsari mai kyau wanda zai kare mutuncin kuri’u tare da bayyana hakikanin ra’ayin masu zabe.
“Dole ne zabukanmu su kasance masu inganci da amincewa kuma sakamakon zaben gwamnan Jihar Osun dole ne ya nuna hakikanin ra’ayin al’umma” in ji Shugaba Tinubu.
Al’ummar Jihar Osun za su fito domin kada kuri’unsu a ranar Asabar 15 ga watan Agusta 2026 domin zaben gwamna daga cikin ‘yan takara 15. Wadannan sun hada da gwamna mai ci Ademola Adeleke dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Asiwaju Munirudeen Bola Oyebamiji da kuma dan takarar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) Najeem Salaam.
LADAN NASIDI



