Kwamitin Yakin Neman Zaben APC Na Tsara Dabarun Samun Nasarar Zaben Gwamnan Osun

Shugaban Kwamitin Yakin Neman Zaben Jam’iyyar APC na Kasa don zaben gwamnan Jihar Osun, wanda kuma shi ne Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya bayyana cewa babban manufar kwamitin ita ce tabbatar da nasarar dan takarar jam’iyyar, Munirudeen Oyebamiji, a zaben gwamnan da za a gudanar a ranar 15 ga watan Agusta.
Da yake jawabi a taron farko na kwamitin yakin neman zaben a Abuja, Uzodimma ya ce ba a tara mambobin kwamitin don yin biki ko shagali ba, sai dai don tsara dabaru da kuma gudanar da ayyukan da za su tabbatar da nasarar APC a zaben.
“Shirinmu shi ne mu je mu tallafa wa ‘yan’uwanmu maza da mata a Jihar Osun domin samun nasara a zaben da ke tafe. Wannan taro ba na nishadi ko shagali ba ne. Taro ne na mutane su zo su bayar da gudummawa da aiki,” in ji shi.

KARANTA KUMA: APC ta Kaddamar da Kwamitin Yakin Neman Zaben Osun
Ya umurci dukkan kananan kwamitocin da ke karkashin babban kwamitin su gudanar da taro nan take tare da gabatar da shawarwari masu amfani da za su karfafa yakin neman zaben jam’iyyar, inda ya jaddada cewa dole ne dukkan ayyuka su kasance masu nufin tabbatar da nasara a zaben.
“Muna da manufa daya tak—ita ce samun nasara a zaben gwamna a Jihar Osun. Za a ajiye sauran batutuwa har sai bayan an kammala zaben. Abu mafi muhimmanci shi ne yin duk abin da zai taimaka mana wajen samun nasara mai gamsarwa a zaben,” in ji Gwamna Uzodimma.
Haka kuma, Gwamnan Jihar Imo ya umurci karamin kwamitin kula da harkokin kudi da ya tsara yadda za a karbi gudummawa daga mambobin jam’iyya da magoya bayanta masu son bayar da tallafi domin daukar nauyin ayyukan yakin neman zaben APC.
A wani bangaren kuma, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa kuma Sakataren kwamitin yakin neman zaben, Barau Jibrin, ya bayyana cewa kwamitin ya kammala taro mai amfani na tsara dabaru, tare da nuna kwarin gwiwar cewa APC za ta sake kwato Jihar Osun.
Ya ce taron ya samu halartar mambobin kwamitin yakin neman zaben da kuma kananan kwamitocinsa daban-daban, inda suka sake jaddada kudirinsu na hadin gwiwa wajen tabbatar da nasarar APC a Jihar Osun.
Jibrin ya bayyana kwarin gwiwar cewa, bisa la’akari da irin goyon bayan da ya bayyana a matsayin mai karfi sosai daga mazauna kananan hukumomi 30 na jihar, .dan takarar jam’iyyar zai samu nasara.
“Tare da wannan gagarumin goyon baya daga al’ummar jihar Osun a dukkan kananan hukumomi 30, muna da kwarin gwiwar cewa, da yardar Allah, dan takararmu, Asiwaju Munirudeen Bola Oyebamiji (AMBO), zai samu nasara,” in ji shi.
Aisha.Yahaya, Lagos