Shugabannin PDP Sun Nemi A Gudanar Da Bincike Kan Takaddamar Shugabanci.

Kungiyar Shugabannin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya (FCT) ta yi kira ga hukumomin tsaro da na tabbatar da doka da su gudanar da bincike kan zarge-zargen kirkirar takardu da kuma bayar da bayanan da ba su dace ba game da hukunce-hukuncen kotu dangane da rikicin shugabancin jam’iyyar.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Abuja ranar Litinin, Shugaban Kungiyar Shugabannin PDP, Hon. Austin Nwachukwu, ya bayyana cewa kungiyar ta ci gaba da jajircewa wajen kare mutuncin jam’iyyar da kuma tabbatar da bin doka da oda.
A cewarsa, shugabannin jihohin sun nuna damuwarsu kan abin da suka kira ci gaba da yunkurin wasu mutane—wadanda kungiyar ta ce an riga an kore su daga jam’iyyar—na bayyana kansu a matsayin wakilan PDP.
“Muna tsaye a gabanku a yau ba don jin haushi ko fushi ba, sai dai don sauke nauyin kare mutuncin PDP, da kare doka da oda, da kuma kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankalin jam’iyyarmu da tsarin dimokradiyyarmu,” in ji shi.
Kungiyar ta nanata cewa sahihin shugabancin PDP shi ne Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC), wanda Shugaban Kasa na Jam’iyya Alhaji Abdulraham Mohammed da Sakataren Kasa Sanata Samuel Nnaemeka Anyanwu ke jagoranta.
“Akwai PDP guda daya tak, wadda hukumar INEC da kotuna suka amince da ita,” in ji Nwachukwu, yayin da yake kira ga hukumomin da abin ya shafa su dauki mataki kan abin da kungiyar ta kira yunkurin bayar da bayanan da ba su dace ba game da shugabancin jam’iyyar.
Shugabannin sun kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su binciki zarge-zargen da suka shafi fassara da kuma bayar da bayanai game da hukunce-hukuncen kotu, tare da jaddada cewa ya kamata a warware matsalolin ta hanyoyin da suka dace da doka.
Domin tabbatar da matsayinta, kungiyar ta ce za ta samar wa manema labarai kwafin hukunce-hukuncen kotun da abin ya shafa, wadanda aka tabbatar da ingancinsu.
Ta kuma yi kira ga tsohon Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan da ya bayyana matsayinsa a fili dangane da rahotannin da ke cewa ana amfani da sunansa a cikin rikicin.
Kungiyar ta kuma yi kira ga Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Mista Nyesom Wike, da ya duba damuwarta game da ayyukan da ake gudanarwa a wani gini da ke Area 10, Garki, Abuja, wanda ta yi zargin cewa ana amfani da shi wajen harkokin da suka shafi rikicin shugabancin.
Bugu da kari, shugabannin jihohin sun bukaci Kwamitin Gudanarwa na Kasa na PDP da su yi amfani da dukkan hanyoyin doka da ake da su domin kare martabar jam’iyyar da kuma tabbatar da bin hukunce-hukuncen kotu da ake da su a duk lokacin da hakan ya zama dole. Dandalin ya bayyana amincewarsa da shugabancin jam’iyyar na yanzu, tare da sake jaddada goyon bayansa ga Kwamitin Gudanarwa na Kasa yayin da yake ci gaba da tafiyar da harkokin jam’iyyar.
Haka kuma, shugabannin sun yi kira ga mambobin jam’iyyar PDP a fadin kasar nan da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu hadin kai, tare da nuna cikakken biyayya ga tsarin da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya shimfida.
“Jam’iyyar PDP ta fi kowane mutum ko gungun mutane girma. Wata kungiya ce da aka gina ta bisa sadaukarwa, bin doka, da kuma ra’ayin jama’a,” in ji Nwachukwu.
Aisha.Yahaya, Lagos



