Afirka

Shugabannin Afirka Sun Tabbatar Da Jajircewarsu Kan Ƙarfafa Bangaren Lafiya

Shugabannin Afirka sun sake jaddada kudirinsu na gina tsarin kiwon lafiya mai juriya a taron musamman na 20 na Majalisar Tarayyar Afirka (AU) kan Lafiya da aka gudanar a Accra Ghana.

 

A cewar sanarwar da aka amince da ita a karshen taron na kwanaki biyu shugabannin Afirka sun amince da rage mace-macen mata da yara da za a iya hanawada  magance cututtukan da ke yaɗuwa da wadanda ba sa yaɗuwa da kuma gina tsarin kiwon lafiya mai juriya a duk faɗin nahiyar.

 

Sanarwar ta kuma yi alƙawarin ƙasashe membobinta su ƙarfafa tsarin samun ingantaccen kiwon lafiya da kuma cimma muradun kiwon lafiya na duniya baki ɗaya nan da shekarar 2030.

 

Yayin da suke alƙawarin ƙarfafa tsarin kiwon lafiya na farko a matsayin tushen tsarin kiwon lafiya mai juriya sun kuma ƙuduri aniyar haɓaka tsarin samar da ayyuka masu inganci ƙarfafa shigar al’umma inganta shirye-shiryen annoba da kuma saka hannun jari a bincike da kirkire-kirkire da kuma kuɗaɗen kiwon lafiya mai dorewa.

 

KARANTA KUMA: Najeriya Ta Amince Da Gyaran da Kungiyar Tarayyar Afirka Ta Shirya

 

Taron ya kuma kuduri aniyar kawar da shingayen kuɗi, tsari, zamantakewa da na yanki ga kiwon lafiya musamman ga mata da yara matasa da nakasassu da ‘yan cirani da mutanen da aka kora da sauran ƙungiyoyi masu rauni.

 

Sanarwar ta kuma sake tabbatar da Sanarwar Abuja wadda ƙasashen Afirka suka kuduri aniyar ware aƙalla kashi 15 cikin 100 na kasafin kuɗinsu na shekara-shekara ga ɓangaren kiwon lafiya don inganta isar da kiwon lafiya ga al’ummarsu yayin da suke haɓaka sabbin hanyoyin samar da kuɗi da rage dogaro da kuɗaɗen waje.

 

A halin yanzu Kwamishinan Lafiya da Harkokin Jinƙai da Ci Gaban Jama’a na AU Ambassador Amma Twum Amoah ya shaida wa taron cewa Afirka ta sami babban ci gaba wajen faɗaɗa hanyoyin samun magani na ceton rai rage mace-macen da suka shafi cutar kanjamau da kuma ƙarfafa tsarin sa ido kan cututtuka.

 

 

LADAN NASIDI

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button