Afirka

Amincewar Al’umma Ta Ƙarfafa Maganin Cutar Ebola A Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kwango

Mutane da yawa na neman maganin cutar Ebola a garin Bunia dake lardin Ituri a Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango inda ake ganin amincewar al’umma na karuwa.

 

Ma’aikatan kiwon lafiya sun bayyana cewa karin mutane na zuwa domin samun kulawa game da wannan cuta mai haddasa zubar jini lamarin da ke saukaka ayyukan kula da su.

 

Dr. Job Kkabagambe Tibasima shi ne mataimakin mai kula da ayyukan Ma’aikatar Lafiya a Cibiyar Kula da masu cutar Ebola ta Evangelical Medical Centre dake Bunia.

 

Ya bayyana hakan a matsayin ci gaba mai kyau a dangantakar da ke tsakanin al’umma da masu bayar da ayyukan kiwon lafiya.

 

“Mara lafiyar da ya zo cibiyar yana samun kulawa yadda ya kamata sannan ya tafi ba tare da wata matsala ba har ma a karshe su kan nuna godiya ga tawagar ma’aikatan lafiyar” in ji shi.

 

Duk da karuwar amincewar da ake samu har yanzu yaduwar cutar Ebola ta fi karfin matakan da ake dauka na tinkararta.

 

An bayar da rahoton mutane sama da 2,500 da suka kamu da cutar zuwa yanzu amma yayin da rashin tsaro da rikice-rikice ke ci gaba da takaita isa ga yankunan da abin ya shafa an kiyasta cewa adadin na iya ninka sau biyu.

 

KARANTA KUMA: Ebola: Afirka CDC Tana Neman Kawo Karshen Haramcin Tafiye-tafiye a Uganda

 

Kodayake yanzu bin diddigin masu kamuwa da cutar ya kai kusan kashi 80 cikin 100 na wadanda aka gano sun kamu da cutar har yanzu kungiyoyi ba za su iya isa ga kowace al’umma ba gano duk wani mara lafiya ko tura kungiyoyin bayar da agaji duk inda ake bukata.

 

Babban fifiko ya kasance rage yaduwar cutar a Ituri ta hanyar karfafa sa ido da binne mutane lafiya da mutunci da kula da lafiya da kuma hadin gwiw ar al’umma.

 

A lokaci guda kuma akwai buƙatar a hanzarta gina ƙarfin mayar da martani a cikin sabbin lardunan da abin ya shafa kafin a kafa tsarin yaɗuwar cutar.

 

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce wannan yana fuskantar ƙalubalen fasaha amma kuma yana buƙatar ɗaukar matakin siyasa don tsagaita wuta don inganta hanyoyin samun agaji da kuma ba da damar hanzarta haɓaka ayyukan.

 

Ta ƙara da cewa mutanen DRC ba za su iya fuskantar barkewar cutar su kaɗai ba. Suna buƙatar tallafi mai ɗorewa daga al’ummar duniya kuma sama da duka suna buƙatar zaman lafiya.

 

LADAN NASIDI

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button