Afirka

Mataimakiyar Shugaban Kasa Ta Farko A Afirka Ta Kudu Ta Rasu

Mataimakiyar shugabar mata ta farko a Afirka ta Kudu Phumzile Mlambo-Ngcuka wacce kuma ta yi aiki a matsayin mataimakiyar sakatare janar ta Majalisar Dinkin Duniya kuma Daraktar zartarwa ta Mata ta Majalisar Dinkin Duniya ta rasu tana da shekaru 71.

Fadar shugaban kasa ta sanar da hakan a daren Juma’a tana mai cewa “An karrama ta saboda gudummawar da ta bayar wajen daidaita jinsi da kuma karfafa wa mata gwiwa.”

An zabe ta a Majalisar Dokoki a shekarar 1994 a matsayin wani bangare na gwamnatin dimokuradiyya ta farko a Afirka ta Kudu tsohuwar malamar ta yi aiki a matsayin mataimakiyar shugaba daga 2005 zuwa 2008.

KARANTA KUMA: Afirka Ta Kudu Ta Kira Jakadan Amurka Kan ‘Dabi’un Diflomasiyya’

Kafin ta zama mataimakiyar shugaba ta yi aiki a matsayin ministar ma’adanai da makamashi da kuma mataimakiyar minista a Ma’aikatar Ciniki da Masana’antu.

A lokacin da take matsayin mataimakiyar shugaba ta kula da shirye-shiryen gwamnati da nufin rage talauci tare da mai da hankali kan mata.

A watan Agusta na shekarar 2013 Mlambo-Ngcuka ta zama Daraktar zartarwa ta UN Women inda ta yi wa’adi biyu a kungiyar wacce ke jagorantar aikin Majalisar Dinkin Duniya kan inganta daidaito tsakanin jinsi da kuma karfafa mata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button