Siyasa

INEC Ta Karfafa Shirye-Shiryen Kayan Aiki Da Dabaru Don Zaɓen 2027 A Jihar Ondo

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a Jihar Ondo ta karbi karin kayan zabe wadanda ba na musamman ba domin karfafa shirye-shiryen gudanarwa na Babban Zaben Najeriya na shekarar 2027.

Kwamishinan Zabe na Jihar (REC) Dr. Mutiu Agboke ne ya karbi kayan a ofishin hukumar na jihar da ke Alagbaka a Akure babban birnin Jihar Ondo.

Kayan sun hada da rumfunan kada kuri’a da muhimman kayan aikin ofis kamar su biro igiyoyi ambulo da tef din mannewa tare da wasu kayayyakin da ake bukata domin gudanar da zabe yadda ya kamata.

Hukumar ta bayyana cewa an ajiye kayayyakin cikin aminci a ofishinta na jiha har zuwa lokacin da za a rarraba su zuwa ofisoshinta da ke kananan hukumomi daban-daban a fadin jihar.

Ana sa ran isowar wasu karin kayan zabe wadanda ba na musamman ba a kwanaki masu zuwa yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen zaben shekarar 2027.

Ci gaba da isar da kayan zaben wani bangare ne na kokarin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ke yi na karfafa karfin gudanar da ayyukanta inganta tsarin tafiyar da kayayyaki da kuma tabbatar da yin cikakkun shirye-shirye kafin babban zaben.

Shirye-shiryen da Hukumar ke ci gaba da yi sun nuna muhimmancin tsara abubuwa tun da wuri da kuma samar da kayan aikin zabe a kan lokaci domin tabbatar da gudanar da zabe mai inganci abin dogaro da kuma tsari mai kyau.

KARANTA KUMA: INEC Ta Horar Da Jami’an Tsaro Gabanin Zaben 2027

Ana sa ran INEC za ta ci gaba da rarraba muhimman kayan aiki da gudanar da sauran shirye-shirye a fadin Jihar Ondo yayin da ake ci gaba da kusantowar Babban Zaben 2027.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button