Najeriya

Shugaba Tinubu ya gana da EFCC da kuma Minista kan gidajen da aka kwace

A ranar Talata Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da Shugaban Zartarwa na Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC) Olanipekun Olukoyede da Ministan Gidaje da Ci Gaban Birane Muttaqha Darma kan kula da kuma zubar da gidajen da aka kwace a fadin kasar.

 

Taron wanda aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke Abuja ya mayar da hankali kan tabbatar da cewa an gudanar da kula da kuma zubar da kadarorin da aka kwace bisa ka’idojin gaskiya da rikon amana.

 

KARANTA KUMA: Shugaba Tinubu Ya Umarci EFCC Da Ta Bude Asusun Jihar Osun

Taron ya jaddada kudirin Gwamnatin Najeriya na bayyana gaskiya da rikon amana wajen kula da kuma zubar da kadarorin da aka kwace a fadin kasar.

 

 

Ladan Nasidi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button