Adadin Masu kamuwa Da Cutar Ebola A Kwangongo ya zarce 5,000

Bayanan gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo sun tabbatar da cewa adadin mutanen da suka kamu da cutar Ebola ya zarce 5,000.
An fitar da wadannan bayanan ne a makare ranar Talata. Jami’an kiwon lafiya sun yi gargadin cewa kokarin da ake yi na shawo kan wannan cuta mai kisa ba ya samun nasara.
KARANTA KUMA: Adadin wadanda suka mutu sakamakon Ebola a DRC ya zarce na annobar baya
Annobar Ebola ta 17 a Congo ta zama mafi girma a tarihin kasar dangane da yawan mutanen da suka kamu da ita a karshen watan Yuli sannan a karshen makon da ya gabata adadin wadanda suka mutu ya kai 2,378—kamar yadda hukumar kiwon lafiyar jama’a ta bayyana—wanda hakan ya zarce adadin wadanda suka mutu a annobar da ta fi muni a baya wato ta shekarar 2018-2020.
Reuters/Ladan Nasidi.



