Jam’iyyar Labour Ta Taya Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan Murnar Cika Shekaru 69

Shugabar jam’iyyar Labour Party ta kasa a Najeriya Sanata Esther Usman ta shiga cikin miliyoyin ‘yan Najeriya wajen taya tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan murnar cika shekaru 69 da haihuwa.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ga manema labarai Sanata Usman ta bayyana tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan a matsayin mutumin da bai taba daina nuna mata goyon baya kauna da alheri ba.
Ta bayyana cewa kauna da alherin da tsohon shugaba Jonathan ya nuna mata tsawon shekaru ba wai mata kadai ya nuna wa ba ne sai dai halaye ne na asali a tare da shi wadanda ya mika ga dukkan ‘yan Najeriya baki daya.
KARANTA KUMA: Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Tsayawa Kai-da-Fata Kan Burin ‘Yan Najeriya
Shugabar ta jam’iyyar Labour Party ta kuma bayyana cewa “Wannan kauna ta musamman da kake da ita ga Najeriya ce ta sa ka sadaukar da burinka na siyasa na kashin kai domin hidimtawa kasarmu.”
Ta kara da cewa “Saboda wannan kauna ta musamman ce ka taba bayyana wa ‘yan Najeriya cewa burinka na siyasa bai kai matsayin da zai sa a zubar da jinin wani dan Najeriya ba kuma lokacin da ya kamata ka tabbatar da abin da ka fada hakika ka tsaya kan wannan ka’ida.”
“A matsayinka na Babban Kwamandan Sojoji ka zabi zaman lafiya a maimakon nuna karfin siyasa ko wasan siyasa” in ji ta.
Ta kara da cewa “Har ma bayan shekaru da barin ofis ba ka daina yin sadaukarwa da kuma hidimtawa bil’adama ta hanyoyi daban-daban ba.”
“Abubuwan da kake ci gaba da yi ta hanyar gidauniyar ‘Goodluck Jonathan Foundation’ inda kake kan gaba wajen fafutukar ganin an samu shugabanci na gari da zabe mai inganci a yankin Afirka ta Kudu da Sahara shaida ce ta sadaukarwarka ta musamman wajen bauta wa Allah da kuma hidimtawa kasa” in ji ta.
Shugabar ta Labour Party ta tunatar da cewa “Kwanan nan musamman a ranar 17 ga watan Nuwamba tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya sake gargadin ‘yan siyasar Najeriya inda ya bukace su da su bari kaunar da suke yi wa Najeriya ta zama jagora a duk abin da suke fada ko suke aikatawa yayin da kasar ke shirin fuskantar babban zaben shekarar 2027.”
“Muna ci gaba da addu’ar cewa ‘yan siyasarmu na yanzu za su fahimci muhimmancin wannan gargadi naka da ya zo a kan lokaci su rungumi zaman lafiya tare da nuna da’a mutunci da kuma kamewa abubuwan da tsarin dimokuradiyyarmu ke bukata yayin da muke kusantar zabe mai zuwa.”
Shugabar jam’iyyar Labour Party ta kasa ta bayyana cewa za ta “Ci gaba da yi muku addu’ar samun yalwar albarkar Allah a rayuwarku da tsawon rai da koshin lafiya da kuma wadata.”
Haka kuma ta ce har yanzu Najeriya na da damar cin gajiyar dimbin gogewa hikima da kuma musamman ma tsananin tausayi da jin kan dan adam da tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya mallaka.



