Yarima William Da Kate Sun Isa Indiya Domin Halartar Lambobin Yabo Na Earthshot

Yarima William da Gimbiya Kate na Burtaniya sun isa Mumbai Indiya don ziyarar kwanaki uku don halartar kyaututtukan Earthshot na shekara-shekara.
Kyautar Earthshot wacce Yarima William ya kafa a shekarar 2020 tana da nufin gano hanyoyin magance sauyin yanayi da kuma bayar da kyautar fam miliyan 1 ga kowanne mutum biyar da suka yi nasara don fadada ayyukansu.
Tafiyar ma’auratan masarautar ta hada da wasan kurket mai hawa biyu da fitaccen dan wasan kurket na Indiya Sachin Tendulkar hawa kan tsarin jirgin ƙasa na Mumbai da kuma ganawa da taurarin Bollywood da ake sa ran za su halarci bikin bayar da kyaututtukan na ranar Talata.
KARANTA KUMA: Birtaniya da Najeriya sun sake tabbatar da kawancen dabarun
Za su kammala ziyararsu da ganawa da Firayim Ministan Indiya Narendra Modi a New Delhi.
Reuters/Aisha.Yahaya, Lagos



