Afirka

Cape Verde Ta Gudanar Da Zaɓen Shugaban Kasa

Al’ummar Cape Verde na kada kuri’u a zaben shugaban kasa inda shugaba mai ci José Maria Neves ke fafatawa da wasu ‘yan takara biyar ciki har da Joana Rosa tsohuwar ministar shari’a kuma mace ta farko a kasar da ta tsaya takarar shugaban kasa.

Neves wanda ya zama shugaban kasa a shekarar 2021 ya taba rike mukamin firaminista na tsawon shekaru 15. Yana wakiltar jam’iyyar African Party for the Independence of Cape Verde (PAICV) wadda ita ce jam’iyyar siyasa mafi dadewa a kasar.

Jam’iyyar PAICV ta lashe kujeru 37 cikin kujeru 72 a zaben ‘yan majalisa da aka gudanar a watan Mayu lamarin da ya ba wa Francisco Carvalho damar zama firaminista.

Babban abokin hamayyar Neves Joana Rosa tana wakiltar jam’iyyar Movement for Democracy (MpD) wadda ta shugabanci kasar na tsawon shekaru 10 kafin zaben ‘yan majalisa na watan Mayu.

Masu sharhi kan harkokin siyasa sun yi hasashen cewa Neves zai samu gagarumin goyon baya a tsakanin ‘yan takara shidan duk da cewa sakamakon zaben zai dogara ne kacokan kan kuri’un da aka kada.

KARANTA KUMA: Cape Verde na Shirin Gudanar da Zaben Shugaban Kasa

A karkashin tsarin siyasar Cape Verde wanda ya hada tsarin majalisa da na shugaban kasa yana da ikon kin amincewa da kudirci (veto power) kuma yana taka rawar mai shiga tsakani a harkokin siyasar kasar.

Siffofin Samar Da  Aiki Ga Matasa A Yaƙin Neman Zaɓe

Rashin aikin matasa da ƙaura sun kasance daga cikin manyan batutuwan kamfen ɗin yayin da ƙasar tsibirin ke ci gaba da ganin matasa suna barin ƙasar don neman damammaki a ƙasashen waje.

Kasar Cape Verde wacce take da nisan sama da kilomita 600 a yammacin babban yankin Afirka tana da yawan jama’a kusan 500,000 yayin da mafi yawan ‘yan ƙasar ke zaune a ƙasashen waje musamman a Amurka da Portugal.

Neves ya yi alƙawarin shirya taron matasa idan ya sami wa’adi na biyu.

Rosa ta yi kira da a samar da manufofi da za su bai wa matasa damar gina makomarsu a ƙasar maimakon ci gaba da barin ƙasar don neman damammaki a ƙasashen waje.

“Ya kamata gwamnati ta ba matasa damar gina makomarsu a nan gida da kuma hana ci gaba da ƙaura daga Cape Verde zuwa ƙasashen waje,” in ji ta.

Kada Kuri’ar Da Sakamakon 

An shirya buɗe rumfunan zaɓe da ƙarfe 8 na safe agogon gida kuma a rufe da ƙarfe 6 na yamma tare da sa ran samun sakamako na wucin gadi a hukumance cikin kwana biyu ko uku.

Idan babu wani ɗan takara da ya samu fiye da kashi 50 cikin 100 na ƙuri’un manyan ‘yan takara biyu za su ci gaba da zaɓen zagaye na biyu da aka tsara yi a ranar 29 ga Nuwamba.

 

 

Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button