
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi alƙawarin sake gina al’ummomin da hare-haren ta’addanci na tsawon shekaru suka shafa a Jihar Filato da sauƙaƙe dawo da mazauna da suka rasa matsuguni da kuma hanzarta ci gaban tattalin arziki a matsayin wani ɓangare na alƙawarin gwamnatinsa na dawo da zaman lafiya da wadata mai ɗorewa tare da shirye-shiryen ƙarfafa waɗannan ƙoƙarin idan aka sake zaɓe shi a wa’adi na biyu a 2027.
Shugaban ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Asabar yayin da yake jawabi ga magoya baya da magoya bayan jam’iyyar a taron gangamin yakin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC don yankin Arewa maso Tsakiya wanda aka gudanar a filin wasa na Jos International da ke Jihar Filato.
Shugaba Tinubu wanda ya amince da mummunan sakamakon rikicin ƙabilanci tun daga 2001 a jihar ya ce gwamnatinsa tana ba da fifiko ga zaman lafiya sake gina al’umma da kuma farfaɗo da tattalin arziki don dawo da rayuwa da kuma samar da damammaki don ci gaba mai ɗorewa.
“Za mu sake gina al’ummominku kuma za mu dawo da ku cikin al’ummarku” Shugaban ya tabbatar wa mazauna da suka rasa matsuguni yana mai alƙawarin yin aiki tare da Gwamnan Jihar Filato Caleb Mutfwang da sauran masu ruwa da tsaki don dawo da matsugunan da abin ya shafa da kuma ba iyalai damar komawa gidajensu lafiya.

KARANTA KUMA: Gyare-Gyaren Tattalin Arziki Na Shugaba Tinubu Sun Kawo Kwanciyar Hankali Ga Tattalin Arzikin Najeriya – Soludo
Shugaban ya yi kira ga mazauna jihar Plateau da su rungumi hadin kai girmama juna da kuma zama lafiya tare wadanda su ne ginshikan da suka wajaba wajen sake gina al’ummominsu karfafa tsaro da kuma samar da ci gaban tattalin arziki.
“Ina rokon ku da ku manta da duk wani bambanci da ka iya kasancewa tsakaninmu; bari mu yi aiki tare domin kasa daya. Bari in tambaye ku ku da kuke tsaye a can shin kuna da katunan zabenku? Kuna da katunan zaben (PVC). Wannan shi ne makamin da zai kai ku ga wadata wannan shi ne taswirar tafiyarku. Ku yi amfani da shi yadda ya kamata ku yi amfani da shi wajen zaben jam’iyyar APC.
“Abin da ya kamata mu samu shi ne wadata ba rudani ko rikici ba. Ba a zabi gwamnatinmu domin ta haifar da cutarwa a tsakaninmu ko kuma domin ta binne mutane ba. Dole ne mu cire mutane daga kangin talauci zuwa ga wadata” cewar Shugaba Tinubu.
Yayin da yake bayyana matakan karfafa zaman lafiya Shugaban ya bayyana cewa jami’an tsaro 1,000 suna samun horo domin inganta tsaron al’umma yayin da aka sayo na’urorin daukar hoto na sa ido (surveillance cameras) domin inganta tsarin gargadin farko tattara bayanan sirri da kuma ayyukan daukar matakan tsaro.
Ya kara da cewa an ba hukumomin tsaro umarnin kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu da kuma karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu domin dakile sake aukuwar hare-hare kare al’ummomin da ke cikin hadari da kuma samar da yanayi mai aminci domin gudanar da harkokin tattalin arziki.

Bugu da ƙari Shugaba Tinubu ya nuna shirye-shiryen inganta filin jirgin saman jihar a matsayin wani ɓangare na inganta ababen more rayuwa da nufin haɓaka haɗin kai da tallafawa ci gaban tattalin arziki.
Da yake tunani kan mahimmancin jituwa tsakanin al’umma Shugaban ya roƙi mazauna yankin da su shawo kan bambance-bambancen ƙabila da addini yana mai jaddada cewa zaman lafiya yana da mahimmanci wajen dawo da noma sake gina rayuwa da haɓaka ci gaban jihar.
“Dole ne mu zauna tare. Dole ne mu yi noma tare. Dole ne mu gina wannan Filato da wannan ƙasa tare” in ji shi.
A kan babban zaɓen 2027 Shugaba Tinubu ya ƙarfafa ‘yan ƙasa da su shiga cikin tsarin dimokuraɗiyya yana mai bayyana Katin Zaɓe na Dindindin a matsayin muhimmin kayan aikin ɗaukar nauyin jama’a.
Ya tabbatar wa mazauna yankin da isasshen tsaro a lokacin zaɓen kuma ya roƙe su da su yi amfani da haƙƙinsu na zaɓe cikin lumana yayin da yake neman goyon bayansu ga ‘yan takarar APC a dukkan matakan gwamnati.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Farfesa Nentawe Yilwatda ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa cika muhimman alkawuran da ya yi wa jihar Plateau. Ya lissafa ayyuka irin su sanya kyamarorin sa ido ayyukan samar da ababen more rayuwa bayar da tallafin NELFUND na Naira biliyan 11 ga dalibai da kuma daukar mutane 1,000 a matsayin masu gadin dazuzzuka domin karfafa tsaro.
Haka kuma Farfesa Yilwatda ya mika tutocin jam’iyyar APC ga ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar a jihohin yankin Arewa-ta-Tsakiya gabanin zaben shekarar 2027.
Bugu da kari Darakta-Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC Sanata Abdulaziz Yari ya bayyana kwarin gwiwarsa kan nasarar jam’iyyar a jihar Plateau a zaben shugaban kasa na 2027. Ya yi nuni da cewa goyon bayan siyasa ayyukan ci gaba da ke gudana da kuma ayyukan da gwamnatin ta aiwatar za su taimaka wajen sake zaben Shugaba Tinubu.
Sanata Yari ya jaddada cewa gwamnatin ta nuna jajircewa wajen ciyar da kasa gaba musamman ta hanyar zuba jari a fannin ababen more rayuwa matakan inganta tsaro da kuma gyare-gyaren tattalin arziki.
Ya bayyana karuwar kudaden da ake rabawa jihohi daga asusun tarayya daga Naira biliyan 786.161 a watan Yunin 2023 zuwa adadin da ya kai tiriliyoyin Naira a yanzu a matsayin shaida ta karuwar kudaden shigar gwamnati.
“Da yardar Allah manyan ‘yan siyasa masu tasiri a jihar Plateau suna nan a gabanku domin ba ku tabbacin cewa nasarar jam’iyyar a jihar Plateau a shekarar 2027 tana nan daram. Shugaba mai girma a yanzu muna magana ne kan kudaden da ake rabawa a matakin tiriliyoyin Naira” in ji Yari.
Darakta-Janar na kwamitin yakin neman zaben ya kuma bayyana cewa batun tsaro yana daya daga cikin muhimman abubuwan da jam’iyyar APC ta sanya a gaba a cikin tsare-tsarenta na yakin neman zabe mai maki takwas wanda aka kaddamar a jihar Jigawa inda ya jaddada kudurin gwamnatin na kare rayukan al’umma da yankunansu.
“Ga ‘yan adawa wannan ita ce takardar bayaninmu wadda shugaban kasa ya kaddamar a Jihar Jigawa. Ɗaya daga cikin manyan abubuwan shine ceton rayuka da al’ummomi. Waɗanda suka ce ba mu da shirin magance rashin tsaro ya kamata su tuna cewa rashin tsaro ya fara ne a lokacinsu kuma ba su yi komai a kai ba tsawon sama da shekaru 20.
“Jam’iyyar za ta ci gaba da ɗaukar alhakin cika alkawuran yakin neman zabenta tana mai nuna kyakkyawan fata cewa za a cimma gagarumin ci gaba a cikin manyan manufofinta na ci gaba nan da shekarar 2031.” Sanata Yari ya ƙara da cewa.



