Duniya

Amurka Na Shirin Bayyana Takunkuman Da Za Ta Kakaba Wa Iran

Amurka na shirin bayyana sabbin matakan tattalin arziki da ke shafar Iran da kuma kasashen da ke ci gaba da cinikayya da Tehran yayin da babban hafsan sojin Pakistan Field Marshal Asim Munir ke ziyarar Tehran domin inganta zaman lafiya a yankin.

 

Sakataren Baitulmali na Amurka Scott Bessent ya bayyana matakan da ake shirin dauka a matsayin wani babban farmakin kudi da ba a taba ganin irinsa ba kan Iran.

 

“Da safiyar gobe ne za a fara wani muhimmin mataki na yaki ta fuskar tattalin arziki—wato babban farmakin kudi mafi girma da aka taba kaddamarwa kan abokin gaba” in ji Bessent.

 

Washington ta yi gargadin cewa kasashe da kungiyoyin da ke tallafawa tattalin arzikin Iran na iya fuskantar sakamako mara dadi duk da cewa ba a riga an bayyana cikakkun bayanai game da matakan ba.

 

Iran ta yi watsi da matsin lamba daga Amurka tare da yin gargadin cewa za ta iya dakatar da fitar da man fetur daga yankin Tekun Fasha idan aka ci gaba da abin da ta kira yakin tattalin arziki.

 

“Idan aka ci gaba da yakin tattalin arziki ba za a fitar da ko digon man fetur daya ba ko ta hanyar Mashigar Hormuz ko kuma daga ko’ina a yankin Tekun Fasha” in ji Sakataren Majalisar Koli ta Tsaron Kasa ta Iran Mohsen Rezaei.

 

 

Reuters/LADAN NASIDI.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button