Wasanni

Hukumar FA Ta Spaniya Ta Haramta Wa Golan Equatorial Guinea Wasanni 12

Kwamitin ladabtarwa na Hukumar Kwallon Kafa ta Spain ya dakatar da mai tsaron ragar Equatorial Guinea Jesus Owono daga buga wasanni 12 biyo bayan wani karo da ya yi wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dan wasan gaba na kungiyar Tenerife Jesus de Miguel.

Owono da De Miguel sun yi karo ne a yayin wani wasa a rukuni na biyu na gasar Spain tsakanin kungiyoyin FC Andorra da Tenerife a ranar 2 ga watan Nuwamba. An garzaya da De Miguel zuwa sashen kula da marasa lafiya masu tsananin rashin lafiya (ICU) inda ya rasu a rana ta biyu.

Kwamitin ya bayyana cewa Owono ya aikata laifi mai tsanani bisa tanadin Sashe na 102 na dokokin ladabtarwa na Hukumar Kwallon Kafa ta Spain wato nuna rashin da’a ta hanyar amfani da karfi da ya haifar da mummunan rauni ga dan wasan da ke fafatawa da shi.

Kwamitin ya sanya masa hukunci mafi tsanani tare da tarar kudi kamar yadda aka tsara a Sashe na 52 na dokokin.

“Bayanin da alkalin wasan ya bayar da kansa ya sa aka fahimci irin tsananin munin abin da ya faru” in ji kwamitin.

“Wannan ya faru ne saboda yadda aka yi abin inda aka daga kafa da kuma karfin bugun wanda alkalin wasan ya bayyana a fili a matsayin wuce gona da iri.”

“Kowa ya sani cewa sakamakon wannan lamari mai ban tausayi shi ne mutuwar Jesus de Miguel Alameda” in ji kwamitin yana mai cewa tsananin munin lamarin ya ba da damar “a sanya hukunci mafi tsauri da za a iya yankewa.”

Owono mai shekaru 25 ya janye daga tawagar Equatorial Guinea da za ta buga wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) da Zimbabwe a wannan watan biyo bayan mutuwar De Miguel.

KARANTA KUMA: Wasannin Neman Cancantar AFCON: Senegal Da Côte D’Ivoire Sun Samu Nasarori Masu Muhimmanci

Kocin kungiyar FC Andorra Carles Manso ya bayyana cewa Owono bai yanke shawara ba tukuna ko zai koma fagen wasa inda ya kara da cewa kungiyar za ta ba mai tsaron ragar lokaci da sarari domin ya yi tunani kan matakin da zai dauka.

A makon da ya gabata Owono ya bayyana cewa yana fuskantar “kwanaki mafi wuya a rayuwata” yayin da Hukumar Kwallon Kafa ta Equatorial Guinea ta bayyana cewa yana cikin tsananin bakin ciki da jimami.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button