Trump Ya Yi Barazanar Ninka Harajin Kayan Maxico Kan Batun Bakin Haure

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar ninka harajin kayayyakin da ake shigo da su daga Mexico idan har kasar ta gaza dakatar da bakin haure sama da 1,000 da ke tafiya zuwa arewa inda ya yi gargadin cewa ba za a bar su su shiga kasar ba.
Trump ya fitar da wannan gargadi a ranar Alhamis ta shafin sada zumunta inda ya bukaci hukumomin Mexico su dakatar da tafiyar wadannan mutane in ba haka ba za a kara harajin kayayyakin Mexico nan take.
“Ga shi nan kuma” in ji Trump. “Ba za a karbe su ba! DOLE ne MEXICO ta dakatar da su YANZU kuma idan ba su yi hakan ba za a NINKA harajin kayayyakin Mexico NAN TAKE.”
Ya kara da cewa an sanar da Mexico, da sabon gwamnan jihar Texas da jami’an tsaron kan iyaka na Amurka da kuma hukumar kula da shige da fice da kwastam (ICE) game da wannan umarni yana mai jaddada cewa ba za a nuna sassauci ba ko kadan.
An kiyasta cewa bakin haure kimanin 1,500 wadanda yawancinsu suka fito daga kasashen Amurka ta Tsakiya sun bar birnin Tapachula da ke kudancin Mexico kusa da iyakar kasar Guatemala a ranar Talata.
KARANTA KUMA: Trump ya yi barazanar sanya haraji kan kasashen da ke adawa da kokarin Amurka na mallakar Greenland
Shugabar kasar Mexico Claudia Sheinbaum ta tabbatar da cewa akwai gungun bakin haure da ke tafiya zuwa arewa amma ta ce babu wata tawagar bakin haure da ta isa kan iyakar Amurka tun bayan da Trump ya dawo kan karagar mulki a shekarar da ta gabata.
Ta ce an sanar da bakin hauren game da kalubalen da ke tattare da shiga Amurka kuma Mexico na duba hanyoyin da za ta bi wajen mayar da su kasashen da suka fito.
“Ba za a yi amfani da karfin tuwo ko danniya ba” in ji Sheinbaum.
Kafofin yada labarai na cikin gida sun rawaito cewa hukumomi a jihar Chiapas da ke kudancin Mexico sun mayar da wasu bakin haure da suka yi kokarin shiga cikin gungun a wannan makon.
Markwayne Mullin wani jami’i a ma’aikatar tsaron cikin gida ta Amurka ya mayar da martani kan gargadin Trump inda ya ce gwamnati za ta yi amfani da dukkan hanyoyin da take da su wajen kare iyakokin kasar.
“Ba za a bari wannan tawagar bakin haure ta shiga kasar tamu ba. Karshen magana” in ji Mullin a shafin sada zumunta.
Wannan barazana ta sanya haraji ta zo ne a daidai lokacin da Amurka da Mexico ke tattaunawa kan yarjejeniyar ciniki bayan da Trump ya ki amincewa a watan Yuli da tsawaita Yarjejeniyar Amurka Mexico Canada (USMCA). Dokar hana shige da fice ta Trump ta rage yawan ‘yan cirani zuwa kan iyakar kudancin Amurka lamarin da ya sa matsugunan ‘yan cirani da dama a Mexico suka zama babu kowa a ciki.
Tsaron kan iyaka babban batu ne a yakin neman zaben shugaban kasa na Trump a shekarar 2024 tare da damuwa game da kwararar bakin haure da suka taimaka wajen komawa Fadar White House.
Bayan zaben tsakiyar wa’adi na 3 ga Nuwamba Trump ya ce yana sa ran sabuwar gwamnan jam’iyyar Democrat da aka zaba a Texas Gina Hinojosa za ta ba da fifiko ga tsaron kan iyaka.
Sai dai Trump ya kuma amince da suka ta fuskar siyasa game da shirin gwamnatinsa na korar mutane wanda hukumar ICE ke aiwatarwa.
A wata hira da aka yi da shi ranar Lahadi Trump ya bayyana aikin korar mutanen a matsayin mai “Tsauri sosai” kuma ya ce a shirye yake ya cimma yarjejeniya kan harkokin shige da fice tare da ‘yan jam’iyyar Democrat a lokacin da za su karbi ragamar Majalisar Dokoki a watan Janairu.



