Hukumar Zaɓen Gambia Ta Tabbatar Da ‘Yan Takara Biyar Domin Zaɓen Shugaban Ƙasa Na Disamba

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Gambia ta tabbatar da ‘yan takara biyar don zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 5 ga watan Disamba, ciki har da shugaba mai ci Adama Barrow wanda ke neman wa’adi na uku a kan karagar mulki.
Hukumar ta sanar da sunayen ‘yan takarar a ranar Alhamis bayan tantance takardun tsayawa takara da masu neman mukamin suka gabatar gabanin zaben.
Sauran ‘yan takarar da aka amince da su sun hada da babban jagoran ‘yan adawa na kasar Ousainou Darboe daga jam’iyyar United Democratic Party da kuma shahararren dan siyasa matashi Talib Ahmed Bensouda daga jam’iyyar UNITE Party.
KARANTA KUMA: Tawagar ECOWAS Za Ta Tantance Shirye-shiryen Zaben Gambia
Jerin sunayen ya kuma kunshi Isatou Touray mace ta farko a kasar da ta tsaya takarar shugaban kasa da kuma Modou Lamin Sima daga jam’iyyar Alliance of Progressive Citizens.
Barrow, wanda ke jagorantar jam’iyyar National People’s Party ya hau karagar mulki a shekarar 2016 bayan ya kayar da tsohon shugaba Yahya Jammeh wanda hakan ya kawo karshen mulkinsa na shekaru 22.
Duk da cewa da farko Barrow ya nuna cewa ba zai nemi wa’adi na uku ba kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1997 bai sanya iyakar wa’adin mulki ga shugaban kasa ba.
Kokarin sanya iyakar wa’adin mulki ta hanyar gyaran kundin tsarin mulki ya ci tura sau biyu bayan da ‘yan majalisa suka yi watsi da sabbin kundin tsarin mulkin da aka gabatar.
Darboe tsohon mataimakin shugaban kasa kuma gogaggen dan siyasar adawa yana kokarin zama shugaban kasa a karo na biyar bayan ya zo na biyu a zabukan da suka gabata.
A daya bangaren kuma, Bensouda tsohon magajin garin Kanifing ya samu goyon baya sosai daga matasa a ‘yan watannin nan.
Burinsa na tsayawa takarar shugaban kasa ya fuskanci rashin tabbas bayan wani rahoton gwamnati ya zarge shi da rashin gaskiya wajen tafiyar da harkokin kudi a lokacin da yake rike da mukamin magajin gari. Sai dai hukumar zabe ta amince da takararsa a yanzu.
Zaben na ranar 5 ga watan Disamba zai kasance zaben shugaban kasa na uku tun bayan da kasar ta koma tsarin dimokuradiyya a shekarar 2016.
Ana sa ran ayyukan yakin neman zabe za su fara a ranar Litinin mai zuwa kuma za su ci gaba na tsawon makonni biyu gabanin ranar zaben.



