Shugaba Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Tsohon Shugaban Jami’ar OAU Omole

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa game da rasuwar tsohon Shugaban Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU) da ke Ile-Ife Farfesa Adebowale Omole. Shugaban ya bayyana shi a matsayin kwararren malami kuma hazikin mai sharhi kan al’amuran jama’a wanda gudummawar da ya bayar ga fannin ilimi da ci gaban kasa za ta ci gaba da kasancewa a tarihi har abada.
A cikin sakon ta’aziyya da ya fitar ranar Alhamis ta hannun Mashawarcinsa na Musamman kan Harkokin Yada Labarai da Dabaru Mista Bayo Onanuga Shugaban ya bayyana bakin cikinsa game da rasuwar wannan fitaccen malami tare da yaba gudummawar da ya bayar wajen gudanar da harkokin jami’a da kuma aikin jarida.
KARANTA KUMA: Shugaba Tinubu Ya Yaba da Zaman Lafiyar da aka samu a Shekaru 31 na Sarautar Sarkin Ilorin
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa Farfesa Omole ya yi fice saboda sadaukarwarsa ga neman ilimi jagoranci a cibiyoyin ilimi da kuma bunkasa ilimi mai zurfi a Najeriya.
“Farfesa Omole ya yi fice a tsakanin masana saboda sadaukarwarsa ga ilimi jagoranci a cibiyoyin ilimi, da kuma ci gaban ilimi mai zurfi a Najeriya” in ji Shugaban.
Ya kuma yi nuni da gudummawar da marigayin ya bayar a fannin aikin jarida a matsayinsa na Shugaban Kwamitin Edita na jaridar The Guardian inda zurfin iliminsa da gogewarsa suka taimaka wajen tsara alkiblar edita ta jaridar.
“Ya kuma bayar da gudummawa ga aikin jarida ta hanyar aikinsa a jaridar The Guardian inda ya yi amfani da dimbin gogewarsa zurfin iliminsa da kuma sadaukarwarsa wajen tsara alkiblar edita ta jaridar” in ji shi.
Shugaba Tinubu ya bayyana rasuwar Farfesa Omole a matsayin babban rashi ga fannin ilimi a Najeriya da masana’antar yada labarai da kuma kasar baki daya.
Shugaban ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin da shugabanni da ma’aikatan jaridar The Guardian da kuma Majalisar Gudanarwa shugabanni ma’aikata da daliban Jami’ar Obafemi Awolowo.
Ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya ba wa Farfesa Omole hutu na har abada kuma Ya bai wa iyalansa abokan aikinsa da dukkan wadanda ke jimamin rasuwarsa hakuri da juriya.



