Zelenskiy Ya Yi Maraba Da Sakonnin Amurka Game Da Warware Yakin Rasha

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskiy ya bayyana cewa sakonnin da ya samu daga Amurka game da kokarin kawo karshen yakin da ake yi da Rasha sun ba shi kwarin gwiwa kuma ana samun ci gaba wajen warware rikicin wanda yanzu ya shiga shekararsa ta biyar.
Da yake magana a wani taron manema labarai a Copenhagen Denmark a ranar Talata da ta gabata Zelenskiy ya bayyana gamsuwarsa da sakonnin da suka fito daga Washington dangane da kokarin kawo karshen yakin.
KARANTA KUMA: Rasha za ta tura manyan jami’ai zuwa tattaunawar zaman lafiya tsakanin Amurka da Ukraine
Zelensky ya ce “Ina ganin sauye-sauye. Ina matukar farin ciki da abin da nake ji” inda ya siffanta ranar farko ta tattaunawar a matsayin mai amfani kuma mai cike da muhimman batutuwa.
Ya kara da cewa “Dukkanmu muna taka tsantsan sosai game da wannan batu domin babu wanda ya fahimci ainihin abin da suke so dari bisa dari. Ina tsammanin mu mun fahimta amma babu wanda ya ga takardun ko kuma abin da Amurkawa suka tattauna da Rashawa.”
Reuters/Aisha.Yahaya, Lagos



