Afirka

Masar Ta Sake Bude Ofishin Jakadancinta A Libya Bayan Shekaru 12

Masar ta sake bude ofishin jakadancinta a Tripoli babban birnin kasar Libya bayan shekaru 12. Matakin na nuni da karfafa alakar diflomasiyya da hukumomin da ke gudanar da harkoki a yammacin kasar.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Masar ta sanar da sake bude ofishin a wata sanarwa da ta fitar a birnin Alkahira lamarin da ke nuna sauyi a dangantakarta da gwamnatin da ke Tripoli.

A baya Masar ta kasance daya daga cikin manyan masu goyon bayan kwamandan sojoji da ke gabashin kasar Khalifa Haftar wanda dakarunsa ke adawa da hukumomin da ke yammacin Libya.

Alkahira ta rufe ofishin jakadancinta a Tripoli a shekarar 2014 a daidai lokacin da ofisoshin jakadancin kasashe da dama suka janye sakamakon tsanantar rikici da kuma bullar gwamnatoci masu adawa da juna a kasar.

KARANTA KUMA: ICAO Ta Dage Takunkumin Sararin Samaniya Da Aka Sanya Wa Libya Tsawon Shekaru Goma

Da yake jawabi a wajen bikin sake bude ofishin Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdelatty ya bayyana cewa muhimmancin tarihi na ginin ofishin jakadancin yana nuni da dadaddiyar alaka tsakanin kasashen biyu.

Ya ce muhimmancin tarihi na ginin “ya yi daidai da zurfaffan alaka ta dan adam da al’adu wadanda su ne ginshikin dangantaka tsakanin Masar da Libya.”

Libya ta fuskanci rashin kwanciyar hankali na siyasa na tsawon lokaci tun bayan hambarar da tsohon shugabanta Muammar Gaddafi a shekarar 2011 sakamakon wani tawaye da kungiyar NATO ta goyi baya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button