Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Sake Jaddada Kudirinsa Na Dorewar Nasarorin Da Aka Samu A Fannin Tattalin Arziki

Shugaba Bola Tinubu ya sake jaddada cewa Najeriya na kan hanyar samun wadata da ci gaban tattalin arziki. Ya bayyana cewa gyare-gyaren da gwamnatinsa ta aiwatar suna haifar da sakamako mai kyau kuma dole ne a ci gaba da su domin karfafa nasarorin da aka riga aka samu.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wajen taron yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC (wanda aka kira ‘Rainbow Coalition’) a Fatakol Jihar Rbas. A wurin ya nuna godiyarsa ga mazauna jihar bisa goyon bayan da suka ba shi a zaben 2023 sannan ya nemi su sake ba shi damar yin wa’adi na biyu a shekarar 2027.

Shugaba Tinubu ya yaba wa al’ummar Jihar Ribas bisa kokarinsu na wanzar da zaman lafiya a tsakiyar rikicin siyasar da jihar ke fuskanta.

Ya yaba wa Gwamna Siminalayi Fubara bisa nuna balagar siyasa yayin da ya bayyana Ministan Babban Birnin Tarayya Nyesom Wike a matsayin abokin aiki mai sadaukarwa wajen ciyar da ayyukan more rayuwa (kayayyakin more rayuwa) gaba a karkashin gwamnatinsa.

KARANTA KUMA: Shugaba Tinubu Ya Isa Jihar Ribas Domin Halartar Taron Yakin Neman Zabe Na ‘Rainbow Coalition’

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa gwamnatinsa na gyara kurakuran gwamnatocin baya wadanda suka bar bashin kudaden fansho da na sallamar aiki (gratuities) da suka kai biliyoyin da tiriliyoyin Naira.

“Wadanda suka shugabanci kasar kafin mu sun bar bashin kudaden fansho da na sallamar aiki da suka kai biliyoyin da tiriliyoyin Naira. Muna biyan wadannan basussuka domin kowace iyali ta samu damar shiga cikin wadatar da ake samu. A yau injiniya mai ritaya yana karbar kudaden sallamarsa mai aikin walda mai ritaya yana karbar fanshonsa kuma malami mai ritaya yana karbar nasa a kan lokaci” cewar Shugaban.

Nasarori

Yayin da yake bayyana nasarorin gwamnatinsa Shugaban Kasa ya yi nuni da karuwar kudaden da ake warewa jihohi biyan bashin kudaden fansho da na sallamar ma’aikata da aka dade ana bi da kuma zuba jari a fannonin ilimi koyon sana’o’i da karfafa matasa a matsayin shaidar tasirin gyare-gyaren da ake gudanarwa.

Shugaba Tinubu ya yi kira ga matasan Najeriya da su mallaki katin zabe na dindindin (PVC) tare da shiga harkokin zaben gama-gari na shekarar 2027 sosai.

Ya jaddada muhimmancin ci gaba da aiwatar da tsare-tsaren gyare-gyaren gwamnatinsa domin tabbatar da makomar tattalin arzikin Najeriya.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana tikitin takarar shugaban kasa na Tinubu da Shettima a matsayin hadakar siyasa mafi karfi a Najeriya.

Yilwatda ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya cancanci wa’adi na biyu domin karfafa gyare-gyaren tattalin arziki da tsare-tsaren ci gaban da gwamnatinsa ta fara.

“Idan shekarar 2027 ta zo, muna son ci gaba da wannan mutum mai kawo gyara kuma mai aiki tukuru a matsayin Shugaban Kasarmu. Shi ya sa wannan hadaka da al’ummar Jihar Ribas ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasa ba suka yanke shawarar yin aiki tare domin goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu” in ji shi.

Farfesa Yilwatda ya bayyana kwarin gwiwar cewa Jihar Ribas za ta ba Shugaba Tinubu kuri’u masu yawa inda ya yi hasashen cewa jihar za ta zama daya daga cikin manyan sansanonin yakin neman zaben sake zaben Shugaban Kasar.

“Idan aka kai watan Janairun 2027 jihar Ribas za ta dauki hankalin kowa. Bisa la’akari da karfin tattara jama’a da Gwamnan jihar Ribas Sir Siminalayi Fubara da Ministan Babban Birnin Tarayya Chief Nyesom Wike da sauran shugabannin siyasa da masu ruwa da tsaki ke da shi muna da yakinin cewa jihar Rivers za ta samar da kuri’u masu yawa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu” in ji Shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Darakta-Janar na Majalisar Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na jam’iyyar APC Sanata Abdulaziz Yari Abubakar ya kalubalanci jihar Ribas da ta samar da akalla kuri’u miliyan 2.3 ga Shugaba Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na 2027. Ya yi nuni da cewa jihar tana da mutane miliyan 3.3 da suka yi rajistar zabe wadanda a cikinsu miliyan 2.8 ne suka karbi katunan zabensu na dindindin (PVC).

Yari ya bayyana kwarin gwiwar cewa jihar za ta iya samar da kashi 75 zuwa 80 cikin dari na kuri’un sannan ya bukaci Ministan Babban Birnin Tarayya Nyesom Wike da masu gudanar da yakin neman zaben da su kara kaimi wajen hada kan jama’a a matakin tushe.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button