Shugaba Tinubu Ya Isa Jihar Ribas Domin Taron Gangamin ‘Rainbow Coalition’

Shugaba Bola Tinubu ya isa birnin Fatakol na jihar Ribas domin halartar taron yakin neman zaben shugaban kasa na ‘Rainbow Coalition’ wanda ke goyon bayan sake zaben Tinubu da Shettima a shekarar 2027.
Shugaban ya isa filin jirgin saman kasa da kasa na Obafemi Jeremiah Awolowo da ke Fatakol inda aka yi masa gaisuwar girmamawa ta musamman tare da sauraron taken kasa.
Ya isa tare da Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima gwamnoni shida daga yankin Kudu-maso-Kudu Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio Shugaban jam’iyyar APC na kasa Farfesa Yilwatda Nentawe da sauran manyan jami’an gwamnati.
Haka kuma shugaban ya samu tarba daga manyan shugabannin siyasa masu ruwa da tsaki a jam’iyyar da magoya baya wadanda suka taru a filin jirgin saman domin tarbar sa a jihar.
KARANTA KUMA: Shugaba Tinubu Ya Isa Kaduna Domin Kaddamar Da Yakin Neman Zaben Zam’iyyar APC
Bayan tarbar da aka yi masa a filin jirgin saman Shugaba Tinubu ya wuce zuwa filin wasa na Adokiye Amiesimaka da ke kan titin filin jirgin sama inda aka gudanar da taron yakin neman zaben na ‘Rainbow Coalition’.
Taron wanda Ministan Babban Birnin Tarayya kuma tsohon Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya jagoranta na da nufin karfafa goyon bayan siyasa inganta hadin kan jama’a a matakin tushe da kuma kara karfin gwiwa da kaimi ga kokarin sake zaben Shugaba Tinubu a zaben gama-gari na shekarar 2027.

Ana sa ran taron zai jawo hankalin magoya baya sama da 70,000 ciki har da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC shugabannin siyasa kungiyoyi masu kawance da kuma mambobin kungiyar ‘City Boy Movement’ daga sassan jihar Ribas da yankin siyasa na Kudu maso Kudu (South-South).



