Siyasa

Uwargidan Shugaban Kasa Ta Yi Kira Ga Jama’a da su Goyi Bayan Sake Zaben Shugaba Tinubu

Mata a yankin Kudu-maso-Gabas na Najeriya sun bayyana goyon bayansu ga takarar Tinubu da Shettima domin wa’adi na biyu inda suka bayyana matsayinsu a kan hangen nesan da suke da shi ga yankin musamman da kuma kasar baki daya.

Wannan ya bayyana ne a yayin taron mata na jam’iyyar APC na yankin Kudu-maso-Gabas da aka gudanar a Enugu inda aka bayyana nasarorin da gwamnatin ta samu. A wajen taron matan sun bayyana cewa Shugaban kasar ya riga ya tabbatar da kwarewarsa ana iya dogaro da shi kuma ya cancanci sake samun damar jagorantar kasar.

Uwargidan Shugaban Najeriya Oluremi Tinubu wacce ta halarci taron ta bai wa mahalarta tabbacin cewa radadin naƙudar haihuwar sabuwar Najeriya mai ƙarfi da tasiri ya wuce.

KARANTA KUMA: Uwargidan Shugaban Ƙasa Ta Kaddamar Da Hedikwatar Yaƙin Neman Zaɓe Na “Gida-gida”
Uwargidan Shugaban Ƙasa Ta Ba Wa ‘Yan Najeriya Tabbacin Alkawarin Shugaba Tinubu Na Kawo Sauyi

“Kamar yadda Shugaban ya fada lokaci ya yi na samun wadata da ci gaba. Kun sani wahalar nakuda ta haihuwa ta wuce. Yanzu lokaci ne na farin ciki da wadata” in ji ta.

Madam Tinubu ta bayyana cewa Najeriya ana gab da shiga wani yanayi na wadata da ci gaba bayan ta jure radadin matakan gyare-gyare sannan ta yi kira ga mata da su goyi bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a kokarinsa na neman wa’adi na biyu.

Ta bai wa jama’a tabbacin cewa Shugaban Kasa ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen gudanar da ayyukan sauya fasalin kasar tare da jaddada cewa jam’iyyar APC jam’iyya ce mai cika alkawari.

Uwargidan Shugaban Kasa ta bayyana cewa ta hanyar shirin ‘Shirin Sabunta Fata’ ta ci gaba da kokarin karfafa mata matasa da kuma marasa galihu ba wai kawai ta hanyar ba su tallafin kudi ba har ma da samar musu da horo kan sana’o’i da kayan aiki inda ta tabbatar da cewa za a ci gaba da gudanar da wadannan ayyuka.

Ƙarfafawa

Domin ƙara ƙarfafa wannan Uwargidan Shugaban Ƙasa ta ƙaddamar da rabon kayayyakin ƙarfafawa ga mata 5000 a jihar a matsayin babban abin da ya fi daukar hankali a taron.

Haka kuma da take jawabi a wurin taron don nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu Gwamna Peter Mba na Enugu Gwamna Nwifuru na Ebonyi da duk sauran ‘yan takarar APC a Kudu maso Gabas na Majalisar Dattawa Wakilai da Majalisar Dokoki ta Jiha sun cika kuma suna  goyon bayan sake zaɓen Shugaba Tinubu.

Matar Shugaban Majalisar Dattawa Matar Kakakin Majalisar Wakilai Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai Gwamnan Jihar Imo Gwamnan Jihar Ebonyi Shugabar Mata ta Jam’iyyar APC ta Kasa da kuma Ministar Harkokin Mata.

Tun da farko Uwargidan Shugaban Kasa da matan da ke cikin jihar sun ziyarci Majalisar Sarakunan Gargajiya ta jihar karkashin jagorancin Igwe Samuel Asadu.

Da yake magana a madadin Sarakunan Gargajiya Igwe ya bayyana cewa “Sun gamsu da manyan nasarorin da Shugaba Bola Tinubu ya samu kuma za su ba shi goyon baya.”

Sun gode wa Uwargidan Shugaban Kasa saboda kokarinta na tabbatar da rayuwa mai kyau ga mata matasa da yara musamman ta hanyar ayyukan da ta gudanar a karkashin shirin ‘Shirin Sabunta Fata’.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button