Shugaba Tinubu Ya Nada Dabiri A Matsayin Kwamishinan Hukumar NASC Mai Wakiltar Yankin Kudu-Maso-Yamma

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Agboola Lukman Dabiri a matsayin Kwamishina mai wakiltar yankin Kudu-maso-Yamma a Hukumar Kula da Ma’aikatan Majalisar Dokoki ta Kasa (NASC).
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a Babban Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Yada Labarai da Dabaru Bayo Onanuga ya bayyana cewa wannan nadi wani bangare ne na kokarin Shugaba Tinubu na karfafa wakilci mai inganci da kuma samar da damar shigar da kowa a cikin Hukumar Kula da Ma’aikatan Majalisar Dokoki ta Kasa.
KARANTA KUMA:http://Shugaba Tinubu Ya Fi Ba da Muhimmanci ga Kammala Ayyuka fiye da Alkawura
Kafin nadin nasa Dabiri ya taba rike mukamin Kwamishinan Matasa da Ci gaban Al’umma a Jihar Legas sannan a baya ya rike mukamin Sakatare mai kula da Tsare-tsaren Tattalin Arziki Samar da Kudaden Shiga da Hadin Gwiwar Gwamnati da Kamfanoni Maso Zaman Kansu a Babban Birnin Tarayya.
Dabiri zai maye gurbin Taiwo Olukemi Oluwa wacce ta yi murabus daga mukaminta a ranar 30 ga watan Maris 2026 domin tsayawa takara a babban zaben shekarar 2027 a mazabar tarayya ta Irewole/Isokan a Jihar Osun.



