NYSC Ya Dage Shirin Shiryarwa Na Rukunin Batch B Stream II Na Shekarar 2026.

Hukumar ta bayyana cewa an dauki wannan matakin ne saboda ayyukan gyare-gyaren da gwamnatocin jihohin biyu ke gudanarwa a sansanonin horarwar.
A cikin wata sanarwa da Daraktar yada labarai da hulda da jama’a ta hukumar, Caroline Embu, ta fitar, an bayyana cewa za a gudanar da bikin karbar mahalarta da kuma bikin rantsarwa a ranar Juma’a, 14 ga watan Agusta, yayin da aka tsara gudanar da bikin kammala shirin a ranar Talata, 1 ga watan Satumba.
KARANTA KUMA: NYSC ta kayyade ranar fara shirin horarwa na rukunin ‘Batch B Stream II’ na 2026
Hukumar NYSC ta shawarci dukkan matasan da aka tura zuwa wadannan jihohi biyu domin shiga shirin (PCMs) da su guji yin tafiya da dare tare da sanya batun tsaron lafiyarsu a gaba yayin da suke kan hanyar zuwa sansanonin horarwar.
Daraktan Janar na hukumar NYSC, Olakunle Nafiu, ya yi wa matasan fatan samun tafiya mai aminci da kuma nasara a yayin gudanar da shirin horarwar.
Aisha.Yahaya, Lagos



