
Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Jama’ar Sin, Jakada AbdulRahman Bello Dambazzau, ya fara gudanar da shawarwari na diflomasiyya bayan karɓar ragamar aikinsa, inda ya fara da jerin ziyarar ban-girma ga takwarorinsa jakadun ƙasashen Afirka da ke birnin Beijing.
A matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa alaƙar diflomasiyya da haɓaka haɗin gwiwa a yankin, Jakada Dambazzau ya kai ziyarar ban-girma ga Jakadan Laberiya a ƙasar Sin, McKinley Thomas, wanda kuma shi ne shugaban jakadun ƙasashen Yammacin Afirka a ƙasar Sin.

Taron ya ba da dama don tattauna batutuwan da suka shafi muradun juna da kuma hanyoyin inganta hadin gwiwa tsakanin ofisoshin diflomasiyya na Afirka ta Yamma a China.
KARANTA KUMA: Jakadan Ya Sake Tabbatar da Karfafa Hulɗar Sin da Najeriya
Jakadan Najeriya ya kuma ziyarci Jakadiyar Seychelles zuwa China, Mrs Anne Lafortune. A lokacin taron, jami’an diflomasiyyar biyu sun yi musayar ra’ayoyi kan batutuwan da suka shafi muradun juna, suna sake jaddada kudurinsu na inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu da kuma bangarorin da suka shafi bangarori daban-daban.
Tattaunawar ta kasance wani bangare na huldar da Jakadan Dambazzau ke yi da al’ummar diflomasiyya a China yayin da yake fara wa’adin aikinsa, don karfafawa da kuma bunkasa dangantaka da abokan huldar Afirka da kuma ciyar da manufofin harkokin waje na kasar gaba.
Aisha. Yahaya, Lagos



