Burkina Faso Ta Yi Kira Da A ƙarfafa Haɗin Gwiwa Tsakanin Rasha Da Afirka

Shugaba Traoré na Burkina Faso ya yi kira da a samar da horo ga matasa a canja fasaha tare da nuna girmamawa ga juna a yayin taron kolin Rasha da Afirka karo na uku da aka gudanar a birnin Moscow.
An gabatar da wannan kira ne a taron kolin Rasha da Afirka karo na uku a birnin Moscow.
Shugaba Traoré yana ba da shawarar cewa ya kamata kawancen da ke tsakanin Rasha da Afirka ya haifar da sakamako na zahiri musamman ta fuskar horar da matasa da kuma canja fasaha.
Firayim Ministan Burkina Faso Rimtalba Jean Emmanuel Ouédraogo ya karanta sakon Shugaba Ibrahim Traoré a yayin wani zama na musamman da ya samu halartar manyan jami’ai a rana ta biyu ta taron.
“Wannan taro na uku ya kamata ya mayar da hankali kan aiwatar da wannan kawance mai Muhimmanci” in ji Shugaba Traoré a cikin sakonsa.
Burkina Faso na son karfafa horar da daliban Afirka a kasar Rasha kan fasahohi na zamani da fannoni masu muhimmanci tare da yin kira ga hadin gwiwa bisa tushen girmamawa ga juna musayar alheri da kuma canja kwarewa.
Shugaban na Burkina Faso ya yi kira da a fadada kawance da bangarori daban-daban domin bai wa kasashen Afirka damar tafiyar da albarkatunsu da kansu da kuma zabar abokan hulwarsu cikin ‘yanci.
Ya kuma yaba da hadin gwiwar da ke tsakanin Burkina Faso Mali da Nijar a karkashin kungiyar kasashen yankin Sahel (AES) tare da jinjinawa kokarin dakarun da ke yaki da kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi.
A fagen kasa da kasa Traoré ya yi kira da a mutunta dokokin kasa da kasa tare da yin garambawul ga cibiyoyin duniya yana mai jaddada cewa ya kamata a dauki Afirka a matsayin cikakken bangare mai tasiri a harkokin duniya.
“Afirka ba ta son zama filin yaki ko ma’ajiyar albarkatun kasa ko kuma kawai kuri’a a cikin taro. Tana son zama kasa mai mutunci da Girma” in ji shi.
Taron kolin Rasha da Afirka karo na uku na da nufin karfafa alaka tsakanin Moscow da kasashen nahiyar Afirka a daidai lokacin da kasashen Afirka ke kokarin fadada kawancen da suke da shi a fannonin tattalin arziki da diflomasiyya.



