Shugaba Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisar Dattawa Kan Lamunin Dala Biliyan 20.52 Da Yuro Biliyan 1.05

Shugaba Bola Tinubu ya nemi Majalisar Dattawa ta amince da wani shiri na karin bashin waje na dala biliyan 20.52 da kuma Yuro biliyan 1.05 na lokacin kasafin kudi na 2026-2027.
Bukatar ta kunsa ne a cikin wata wasika da aka aika wa Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio kuma aka karanta a zaman taron majalisar a ranar Talata fa ta gabata.
Tinubu ya ce za a tura rancen da aka tsara zuwa muhimman sassan tattalin arziki ciki har da kayayyakin more rayuwa noma kiwon lafiya ilimi samar da ruwa tsaro samar da ayyukan yi da kuma gyare-gyaren kula da harkokin kudi.
A cewar Shugaban an yi niyyar shirin rancen ne don magance gibin kayayyakin more rayuwa na Najeriya da kuma cike gibin kudi da ake bukata don aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba a fadin kasar.
Ya bayyana cewa an zabi ayyukan da shirye-shiryen da aka kama a cikin shirin ne bayan kimanta fasaha da tattalin arziki tare da la’akari da gudummawar da ake sa ran za su bayar ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya.
“Waɗannan shirye-shiryen suna da nufin samar da aikin yi inganta samun ƙwarewa haɓaka kasuwanci rage talauci da kuma inganta tsaron abinci, duk wanda ke inganta rayuwar yaran Najeriya,” in ji shi.
KARANTA KUMA: Majalisa Ta Goyi Bayan Tsarin Lamunin Shugaba Tinubu
Shugaban ya kara da cewa mafi yawan ayyukan da shirye-shiryen za a aiwatar a fadin jihohi 36 na tarayya da Babban Birnin Tarayya (FCT).
Ya jaddada cewa zuba jari mai yawa a fannin ababen more rayuwa ya kasance dole don haɓaka ci gaban tattalin arziki da magance ƙalubalen ci gaba da aka daɗe ana fuskanta.
“Saboda buƙatar saka hannun jari mai yawa a cikin kayayyakin more rayuwa a ƙasar da kuma dimbin albarkatun kuɗi da ake buƙata don magance wannan gibin ya zama dole a bi diddigin basussukan waje masu kyau don cike gibin kuɗaɗen,” in ji Tinubu.
Ya kuma bayyana cewa za a tura kuɗaɗen musamman zuwa manyan ayyukan samar da ababen more rayuwa musamman a fannin wutar lantarki sufuri da kiwon lafiya.
Tinubu ya roƙi Majalisar Dattawa da ta yi la’akari da buƙatar cikin gaggawa yana mai cewa amincewa za ta ba wa Gwamnatin Tarayya damar cika wa’adinta ga ‘yan Najeriya ta hanyar rarraba kuɗaɗen kan lokaci da kuma aiwatar da ayyukan yadda ya kamata.
Da yake mayar da martani Akpabio ya ce shirin lamunin ya riga ya bayyana a cikin tsarin lamunin da Gwamnatin Tarayya ta amince da shi.
Daga nan sai ya tura buƙatar Shugaban Ƙasa ga Kwamitin Majalisar Dattawa kan Basussukan Cikin Gida da na Ƙasashen Waje don ƙarin nazari kan dokoki tare da haɗin gwiwar Kwamitin Kasafin Kuɗi da Kuɗi.
“An haɗa da shirin rancen amma ba shakka an riga an amince da wannan a cikin kasafin kuɗinmu kuma an amince da shirin rancen waje tun daga 2025 zuwa 2027,” in ji Akpabio.
Aisha.Yahaya, Lagos



