Duniya

Guguwar Champi Ta Kashe Mutum Daya Ta Kuma Jikkata Sama Da Mutane 500 A Taiwan

Guguwar Champi ta ratsa Taiwan inda ta kashe mutum ɗaya tare da raunata sama da 500 yayin da ta rusa bishiyoyi ta kuma katse hanyoyin samar da wutar lantarki.

Guguwar ta ci gaba da raguwa yayin da take tafiya arewa zuwa gabar tekun China kodayake ba a tsammanin za ta sauka a can ba.

A cewar Hukumar Kula da Yanayi ta Tsakiya ta Taiwan (CWA) wata guguwa mai karfi kuma daya daga cikin guguwa mafi karfi a yankin Pacific a wannan shekarar Champi tana raguwa duk da cewa har yanzu tana dauke da iska mai karfin kusan kilomita 126 (78 mph) kusa da tsakiyarta.

CWA ta ce guguwar ta kai kimanin kilomita 170 (mil 106) a arewa maso gabashin Taiwan bayan ta leka gabar tekun arewa maso gabashin tsibirin a gundumar Yilan da sanyin safiyar Asabar.

Tsakiyar guguwar ta juya kudu da misalin tsakar dare ta rungume gabar tekun Yilan kafin ta yi zagaye mai ban mamaki a bakin teku ta kuma koma arewa.

Iska ta bugi kilomita 227 (141 mph) a wasu yankunan bakin teku ta lalata layukan wutar lantarki ta kuma sa tayal din rufin ya tashi.

Tsarin hasashen guguwar ya nuna cewa za ta juya zuwa arewa ta bi sahun gabar tekun China sannan daga karshe ta nufi kudancin Japan.

KARANTA KUMA: Japan Ta Yi Gargadin Ruwan Sama Kamar Da Bakin Kwarya Yayin Da Guguwa Ke Matsowa

Hukumar kashe gobara ta Taiwan ta bayyana cewa adadin wadanda suka mutu ya tsaya a mutum 1 wani mutum da raƙuman ruwa suka tafi da shi daga tsibirin Liuqiu yayin da mutane 527 suka samu raunuka sakamakon iska mai karfi da ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Kamfanin wutar lantarki na Taipower ya ce gidaje sama da 288,000 sun rasa wutar lantarki duk da cewa an riga an dawo wa yawancinsu da wutar.

Ma’aikatar sufuri ta bayyana cewa an soke jiragen sama guda 259 wannan ci gaba ne idan aka kwatanta da ranar Juma’a lokacin da adadin ya kai kusan 1,000.

Ma’aikatar kula da ayyukan gaggawa ta kasar Sin ta tura tawaga zuwa lardin Zhejiang da ke gabashin kasar yayin da guguwar Champi ke matsowa inda ta yi gargadin cewa za a samu iska mai karfi da ruwan sama mai yawa har zuwa ranar Lahadi.

Ma’aikatar ta ce ta tanadi ma’aikatan ceto guda 400 da kayan aiki guda 600 yayin da jami’an kashe gobara sama da 41,000 ke kan aikin gaggawa.

Reuters/ Sulaiman Ibrahim Muhammad

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button