Cinikayyar Afirka Ta Kudu Da Sin Ta Karu Da Kashi 24 Cikin Dari

Cinikin da Afirka ta Kudu ke yi da China ya karu da kusan kashi 24 cikin 100 a kowace shekara zuwa kusan dala biliyan 15 bayan da Beijing ta gabatar da wani shiri na wucin gadi na sifirin haraji ga fitar da kayayyaki daga Afirka da suka cancanta a watan Mayu.
Jakadan China a Afirka ta Kudu Wu Peng ya bayyana hakan a ranar Alhamis yana mai cewa fitar da kayayyaki daga Afirka ta Kudu zuwa China ya karu da kusan kashi 25 cikin 100 zuwa dala biliyan 5.3 yayin da shigo da kayayyaki daga China ya karu da kashi 23 cikin 100 zuwa dala biliyan 9.47 tsakanin Mayu da Agusta.
Ya ce fitar da kayayyakin noma daga Afirka ta Kudu zuwa China shi ma ya sami gagarumin ci gaba wanda ya kai kusan dala miliyan 500 a wannan lokacin wanda ya karu da sama da kashi 35 cikin 100 a shekara.
KARANTA KUMA: Manufar Sin Ta Sifirin Tariff Ta Inganta Fitar Da Kayayyakin Afirka
Ci gaban wani bangare ne na kokarin Afirka ta Kudu na fadada kasuwannin fitar da kayayyaki a tsakanin tsamin dangantaka da Amurka da kuma yiwuwar kara takunkumin ciniki.
Da yake jawabi a wurin taron manema labarai Ministan Ciniki da Masana’antu na Kasar Afirka ta Kudu Parks Tau ya bukaci ‘yan kasuwa na gida da su yi amfani da damar shiga kasuwar Sin ba tare da haraji ba.
Tau ya ce gwamnati za ta ci gaba da tattaunawa don tabbatar da dorewar masu fitar da kayayyaki yayin da take kare masana’antun cikin gida.
Kodayake Washington ta tsawaita Dokar Ci Gaban Afirka da Dama (AGOA) wacce ke bai wa kasashen Afirka wadanda suka cancanta damar shiga kasuwar Amurka ba tare da haraji ba har zuwa shekarar 2028 Afirka ta Kudu na fuskantar barazanar korar baki.
Shugaban Amurka Donald Trump ya soki wasu manufofin cikin gida da na waje na Afirka ta Kudu.
Gwamnatinsa ta kuma zargi gwamnatin Afirka ta Kudu da tsananta wa fararen fata ‘yan Afirka zargin da Pretoria ta musanta.



