
Yawancin ‘yan majalisar dokokin Greenland sun nuna goyon bayansu ga yarjejeniyar tsaro da aka kulla kwanan nan tsakanin wannan tsibiri na yankin Arctic da Shugaban Amurka Donald Trump yayin wata muhawara a majalisar.
Amurka Denmark da Greenland sun rattaba hannu kan yarjejeniyar a watan da ya gabata domin rage tashin hankali bayan barazanar da Shugaba Trump ya rika yi akai-akai na son mallakar tsibirin, wanda ke da muhimmancin dabarun soja da kuma arzikin ma’adanai.
Yarjejeniyar na bukatar a sake duba ta a karo na biyu a majalisa kafin a kada kuri’a a kanta inda ake sa ran ‘yan majalisar za su amince da dokar.
KARANTA KUMA: Shugaba Trump na shirin rattaba hannu kan yarjejeniyar soja ta Greenland
Yarjejeniyar na fadada rawar da sojojin Amurka ke takawa a Greenland, inda za ta ba da damar kafa sabbin sansanonin soja guda biyu da kuma tsarin kare kai daga makamai masu linzami na Shugaba Trump mai suna “Golden Dome,” tare da tabbatar da ikon mallakar kasar Denmark da kuma ‘yancin al’ummar Greenland na yanke hukunci kan makomarsu.
Sai dai shugaban jam’iyyar adawa ta Naleraq, Pele Broberg ya bayyana cewa akwai cikakkun bayanai da dama da ba su da tabbas game da yadda yarjejeniyar za ta yi aiki a zahiri.
“An bai wa Amurka manyan hakkoki a kasarmu. Ba a bai wa al’ummar Greenland garantin samun takamaiman biyan kudi ba don wadannan hakkoki,” in ji Broberg yayin muhawarar majalisar a birnin Nuuk, babban birnin Greenland.
Jam’iyyun da ke mulki wadanda ke da rinjayen kujeru a majalisa sun kare yarjejeniyar.
Tsohuwar Ministar Harkokin Waje Vivian Motzfeldt daga jam’iyyar Demokraatit da ke cikin kawancen masu mulki ta jaddada cewa Greenland ta samu kariya mai karfi ba tare da ta biya komai ba, tare da samun karbuwa a matsayin kasa mai cin gashin kanta.
Ministan Harkokin Waje Mute Egede ya bayyana yarjejeniyar a matsayin babban ci gaba wanda ba za a iya auna shi da kudi ba.
Shugaban jam’iyyar Siumut Erik Jensen shi ma ya tabbatar da goyon bayan jam’iyyarsa ga yarjejeniyar.
“Tsawon shekaru da dama Siumut ta yi ta yakin neman ganin cewa ba a sake kulla yarjejeniyoyi game da Greenland ba tare da sa hannun Greenland ba… Shi ya sa muke gamsuwa,” in ji Jensen.
Reuters/Aisha.Yahaya, Lagos



