Afirka

Mutane 139 Masu Kaura Sun Mutu Bayan Jirgin Ruwansu Ya Kife A Kusa Da Djibouti.

Mutane akalla 139 ciki har da yara 15 sun mutu bayan wani jirgin ruwa na masu hijira ya kife a daren da Ta gabata a gabar tekun Djibouti yayin da suke kan hanyar zuwa Yemen.

Hukumar Kula da Masu Hijira ta Duniya (IOM) ta bayyana cewa mutane 82 wadanda dukkaninsu ‘yan kasar Habasha ne sun tsira yayin da wasu mutane 84 kuma har yanzu ba a san inda suke ba.

Safiya Ibrahim mai kula da ayyukan agaji a hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce jirgin ya kife ne a kusa da garin tashar jiragen ruwa na Obock.

“A cikin jirgin akwai mata da maza, har ma da yara. Adadin wadanda suka mutu ya yi yawa sosai,” in ji ta.

“Wadanda suka tsira sun gaya min cewa jirgin ya fara nutsewa ta baya ne da zarar sun shiga cikinsa,” in ji shugaban ayyukan IOM a Djibouti Alexandre Coissac.

Coissac ya ce: “Muna tare da wadanda suka tsira da kuma iyalan da suka rasa masoyansu ko kuma wadanda har yanzu ba su samu labarin ‘yan uwansu ba.”

An ga wasu kayayyaki na sirri wadanda ake kyautata zaton na mutanen da ke cikin jirgin ne a bakin teku yayin da ake ci gaba da ayyukan neman wadanda suka bata da kuma ceto.

IOM ta ce tana ba da tallafi ga wadanda suka tsira ciki har da kula da lafiyarsu da kuma taimaka musu wajen tuntuɓar iyalansu.

Coissac ya ce wannan bala’i “jan hankali ne mai karfi” game da hadarin da masu hijira ke fuskanta yayin neman sabuwar rayuwa a wasu wurare.

Ya ce daya daga cikin wadanda suka tsira ya gaya masa cewa sun fito ne daga yankin Tigray na arewacin Habasha inda ‘yan tawaye ke gwabzawa da gwamnatin tarayya sakamakon sake barkewar rikici a baya-bayan nan.

Har yanzu kasar Yemen na fama da mummunan yakin basasa, amma duk da wannan rikici da kuma karuwar rashin kwanciyar hankali a yankin baki daya, masu hijira na ci gaba da ketare mashigin ruwa na Bab el-Mandeb.

Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce dubban masu hijira daga yankin Kahon Afirka (Horn of Africa) ne ke yin wannan tafiya mai hadari a kowace shekara, da fatan isa kasashen Gulf domin samun tsaro da kuma aiki.

 

Labaran Afirka/Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button