UTME ta 2026: An Karrama ‘Yan ƙasa Da Shekara 16 Da Wasu Kan Samun Sakamako Mafi Kyau

Gwamnatin Najeriya ta karrama wadanda suka yi fice a jarabawar shiga manyan makarantu ta UTME ta shekarar 2026 ciki har da wasu hazikan dalibai da ba su cika shekaru 16 ba domin nuna godiya ga nasarorin da suka samu a fannin ilimi da kuma damar da suke da ita ta ciyar da kasa gaba.
Ministan Ilimi Dr. Maruf Tunji Alausa da Shugaban Hukumar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) Farfesa Segun Aina ne suka mika kyaututtuka da takardun shaida ga wadannan dalibai a wani biki da aka gudanar a Abuja.
Alausa ya bukaci wadanda suka samu kyaututtukan da su duba fiye da takardun shaidar ilimi kawai su kuma yi amfani da iliminsu wajen samar da mafita ta zahiri ta hanyar kirkire-kirkire, bincike da kuma harkokin kasuwanci.
KARANTA KUMA: http://UTME ta 2026: JAMB Ta Gargadi Dalibai Kan Aikata Laifuka a Lokacin Jarabawa
“Ku ne wakilan makomar kasarmu. Ku ne za ku canza Najeriya da duniya baki daya ta hanyar kirkire-kirkirenku” in ji shi.
“Najeriya na bukatar tsara matasa irinku wadanda za su iya sauya ilimi zuwa kayayyaki ayyuka, da dabaru masu inganta rayuwar al’umma karfafa masana’antu da kuma magance matsalolin zamantakewa da ke damun al’umma.
“Muna sa ran kuma muna fatan ganin kun zama mutanen da za su samar da sabbin dabaru da mafita wadanda za su shafi rayuwar miliyoyin mutane a Najeriya da kuma daruruwan miliyoyin mutane a duniya baki daya” in ji shi.
Ministan ya bayyana cewa bunkasa matasa na daya daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta sa gaba inda ya lura cewa kusan kashi 70 cikin dari na al’ummar Najeriya matasa ne da ba su kai shekaru 30 ba.
Dangane da batun shigar da kananan yara manyan makarantu Alausa ya bayyana cewa daga cikin dalibai kusan 39,000 da suka rubuta jarabawar UTME kuma ba su kai shekaru 16 ba mutane 108 ne kawai suka cika sharuddan shiga manyan makarantu.
Ya ce fiye da dalibai miliyan biyu ne suka rubuta jarabawar yayin da dalibai 391 kacal daga cikin wadanda ba su kai shekaru 16 ba ne suka samu maki 320 ko sama da haka daga cikin 400 wato kashi 80 cikin dari. Bayan an gudanar da karin tantancewa adadin wadanda suka cancanta ya koma 108.
A cewar ministan dole ne ‘yan takara su samu maki aƙalla kashi 80 cikin 100 a jarabawar UTME jarabawar tantancewa ta jami’a (post-UTME) da kuma jarabawar kammala sakandare (O’Level) tare da nuna cewa suna da shiri na tunani motsin rai da hankali domin shiga jami’a.
Alausa ya bayyana cewa an tsara manufar ƙarancin shekarun shiga jami’a ne domin tabbatar da cewa ɗaliban za su iya dacewa da buƙatun karatu da na zamantakewa a rayuwar jami’a. Ya yi kira ga cibiyoyin ilimi da su samar da yanayi mai kyau wanda zai bai wa matasan ɗalibai damar yin karatu da kuma samun nasara ta musamman.
Ya jaddada cewa samun maki mai yawa a jarabawa kaɗai bai isa ya tabbatar da cewa ɗalibi ya shirya domin shiga jami’a ba. Ya ƙara da cewa shugaban hukumar JAMB Farfesa Aina ya gamsu sosai da yadda ɗaliban suka ba da amsoshi yayin aikin tantancewa.
Daga cikin waɗanda aka karrama akwai Owoeye Daniella Jesudunsin daga Jihar Ekiti wacce ta samu maki 372 Enwere Kingsley Ikenna daga Jihar Imo wanda ya samu 370 Olabiyisi Olanrewaju Oluwatimileyin daga Jihar Oyo Victor-Onyeka Daniel Ifeanyi daga Jihar Imo da Osagiobare Daniel Osaherumwen daga Jihar Edo waɗanda kowannensu ya samu maki 368 da kuma Azike Kenechukwu Anthony daga Jihar Anambra wanda shi ma ya samu maki 368.
Dukkan ɗaliban da aka karrama sun sami allunan girmamawa da takardun shaida. Alausa ya taya su murna tare da bayyana kwarin gwiwar cewa basirarsu za ta iya haifar da manyan nasarori da za su inganta rayuwar miliyoyin mutane.



