Ebola: Kwamitin Shugaban Kasa Na Musamman Ya Tabbatar Wa ‘Yan Najeriya Cewa Suna Cikin Shiri

Kwamitin Musamman na Shugaban Kasa kan Shirye-shiryen Yaki da Cutar Ebola da Barazanar Lafiyar Al’umma ya ba wa ‘yan Najeriya tabbacin cewa kasar tana da shiri da kuma karfin da za ta iya dakile cutar Ebola yadda ya kamata. Hakan ya biyo bayan karfafa tsarin sa ido kan lafiyar jama’a inganta hanyoyin daukar matakan gaggawa da kuma aiwatar da matakan takaita yaduwar cutar.
Shugaban kwamitin wanda kuma shi ne Babban Sakataren Fadar Shugaban Kasa (Chief of Staff) Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron gaggawa da kwamitin ya gudanar a Fadar Shugaban Kasa.
Gbajabiamila ya bayyana cewa kwamitin ya kasance yana aiki a boye tun bayan kaddamar da shi a watan Yunin wannan shekarar.
Ya jaddada cewa saboda wannan aikin ne ya sa aka samu damar gano mutum na farko da aka gano yana dauke da cutar a jiya.
“Yana da matukar muhimmanci a lura da wannan. Tun lokacin da batun Ebola ya taso a watan Yuni an samu zirga-zirgar jiragen sama kusan 44,000 da suka shiga ko suka fita daga Najeriya. Don haka nasarar ta samo asali ne sakamakon kokarin da Ma’aikatar Lafiya kwamitin musamman da sauran hukumomin da abin ya shafa suka yi. Kowa ya bayar da gudummawarsa.
“Fasinjan da ke dauke da cutar bai nuna alamun rashin lafiya ba a lokacin da ya isa Abuja alamun sun bayyana ne bayan kwana hudu amma tsarin tantancewa da ka’idojin da aka shimfida su ne suka ba da damar gano shi da wuri. Wannan yana nuna karfin kasar da kuma iyawarta wajen tunkarar wannan cuta yadda ya kamata” in ji shi.
Ya ba wa ‘yan Najeriya tabbacin cewa kwamitin zai kara karfafa duk abin da ke bukatar karfafawa ciki har da ka’idojin aiki tare da tabbatar da cewa an aiwatar da su sosai a nan gaba.
“Kwamitin yana kan aikin yadda ya kamata. Hukumar NCDC ma tana kan aikin kowa yana bayar da gudummawa. Dole ne mu gina amincewar al’umma tare da guje wa firgici. Haka kuma yana da muhimmanci a bayyana karara cewa wannan kokari ne na hadin gwiwa tsakanin gwamnati da al’umma.”
Ya yi kira ga dukkan ‘yan Najeriya da su bi umarnin da aka bayar domin amfanin kowa da kowa. Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a Farfesa Mohammed Ali Pate ya bayyana a cikin wata sanarwa da mai ba Shugaban Kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru Mista Bayo Onanuga ya sanya wa hannu cewa Najeriya tana da hukumomin kiwon lafiya masu kwarewa ciki har da masu gudanar da asibitoci masu zaman kansu da sauran hukumomi tare da hadin gwiwar sassan Shige da Fice Sufurin Jiragen Sama Harkokin Cikin Gida da hukumomin jihohi wadanda suka kafa tsarin sa ido a fadin kasar kuma suna cikin shirin ko-ta-kwana domin daukar matakan da suka dace.
Muna gudanar da aikin gano mutanen da suka yi mu’amala da wanda ya shigo da cutar cikin kasar nan tare da killace su. Za mu ci gaba da yin hakan kuma muna son tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatin tarayya tare da abokan hulɗarta na fasaha wato Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) Cibiyar Kula da Cututtuka ta Afirka (Africa CDC) da kuma Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC)sun kunna tsarin gudanar da lamarin a dukkan bangarorin da abin ya shafa.
“Suna aiki tukuru dare da rana kuma mun shirya asibitocinmu domin mu samu damar shawo kan wannan lamari kamar yadda aka yi a wasu kasashen amma ba za mu yi kasa a gwiwa ba. Ya kamata al’ummarmu su bi umarnin da aka bayar domin kare lafiyar jama’a” in ji shi.
Sauran mambobin kwamitin da suka halarci taron sun hada da Shugabar Hukumar Shige da Fice ta Najeriya Kemi Nandap Shugabar Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Tarayya (FAAN) Bunmi Kuku Babban Manaja a FAAN, Adamu Adamu Wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) Pavel Ursu da kuma Wakilin Musamman na Shugaban Cibiyar Kula da Cututtuka ta Afirka (Africa CDC) Dr. Aliko Ahmed.
Haka kuma akwai Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Gudanarwa da Ayyuka wacce kuma ita ce Sakatariyar kwamitin Oyinade Nathan-Marsh Kwararriya a fannin Lafiyar Jama’a Niniola Williams Sakatariyar Lafiya da Muhalli ta Babban Birnin Tarayya (FCT) Dr. Dolapo Fasawe da kuma Shugabar Kwamitin Ba da Shawara kan Harkokin Kiwon Lafiya a Asibitin Fadar Shugaban Kasa Dr. Victoria Ogala.
Ministar Masana’antu Kasuwanci da Zuba Jari Olajumoke Oduwole Kwamishinan Lafiya na Jihar Legas Farfesa Akin Abayomi da kuma Daraktan Ayyuka Lasisi da Ka’idojin Horarwa (DOLTS) a Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya Kyaftin Donald Spiff su ma sun halarci taron ta hanyar manhajar Zoom.



