Zelenskiy Na Neman Ganawa Da Amurka Da Rasha A Taron Kolin G20

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskiy ya bayyana fatansa na ganawa da wakilan Amurka da na Rasha a gefen taron kolin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki (G20).
Zelenskiy ya shaida wa manema labarai ta hanyar tattaunawa a manhajar WhatsApp cewa, “Ana iya gudanar da taron a Amurka yayin taron kolin na G20. Sai dai har yanzu babu wani tabbaci daga bangaren Rasha ko na Amurka. Haka kuma, ana iya gudanar da shi a wata kasa ta Turai.”
Ya kara da cewa, “Ana iya gudanar da taron a daya daga cikin kasashen Gabas ta Tsakiya. Amurka ta sha ambaton kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa ko Saudiyya a matsayin wuraren da za a iya yin hakan.”
KARANTA KUMA: Tattaunawar Amurka da Rasha kan Ukraine ta fadada zuwa yarjejeniyar man fetur ta biliyoyin daloli
Zelenskiy ya ce wakilan Ukraine sun tattauna da jami’an Amurka a ranar Juma’a, da ta gabata amma bai bayar da karin bayani ba. Ya kuma bayyana cewa Turai na bukatar nata tsarin daban na tattaunawa da Rasha.
Kungiyar kasashe 20 masu karfin tattalin arziki (G20) — wadda ta kunshi Amurka da Rasha amma ba ta hada da Ukraine ba — na shirin gudanar da taron kolinta a birnin Miami a watan Disamba.
Reuters/Aisha.Yahaya, Lagos



