Uwargidan Shugaban Kasa Ta Yi Kira Da A Kara Tallafa Wa Marasa Galihu

Uwargidan Shugaban Najeriya Oluremi Tinubu ta yi kira da a kara bayar da tallafi ga marasa galihu a cikin al’umma.
Ta yi wannan kiran ne a cikin wani sako da ta fitar a ranar Asabar domin tunawa da Ranar Kawar da Talauci ta Duniya ta shekarar 2026.
Ta ce “Ranar Kawar da Talauci ta Duniya ta shekarar 2026 mai taken ‘Mutunci Damammaki da Wadata ga Kowa’ tana tunatar da mu nauyin da ya rataya a wuyanmu na gina al’ummar da kowane mutum zai iya rayuwa cikin mutunci da bege ya sami damammaki masu amfani kuma ya ci gaba don cimma cikakken karfinsa da iyawarsa.”
Uwargidan Shugaban kasar ta kuma ba da shawarar cewa ya kamata a bai wa iyalai masu rauni damammaki daidai da na sauran mutane domin su sami damar amfana da ayyukan jin dadin jama’a da za su inganta rayuwarsu.
KARANTA KUMA: Oluremi Tinubu Ta Bukaci Matasan Musulmi Da Su Yi Amfani Da Damammakin Da Ke Akwai A Duniya
Ta ce ”Dole ne mu ci gaba da fadada damar samun ilimi kiwon lafiya kwarewa hanyoyin samun abin dogaro da kai mai kyau da damammakin tattalin arziki musamman ga iyalai masu rauni.”Ta kara da cewa “Ta hanyar nuna tausayi daukar matakai masu inganci da ci gaba da hadin gwiwa za mu iya samar da hanyoyin fita daga kangin talauci zuwa ga wadata ga kowa.”



