Najeriya

Ministan FCT Ya Zargi NLC Da Sanya Siyasa A Yajin Aikin Malamai Na FCT.

Zantawa da manema labarai a Abuja ranar Talata da ta gabata inda ya yi nuni da cewa muradun siyasa—ba batutuwan da suka shafi walwalar ma’aikata ba—ne suka haifar da wannan yajin aiki da ya kawo cikas ga harkokin koyarwa da karatu a makarantun gwamnati.

Ya kuma yi tambaya game da alakar siyasa ta shugaban NLC na FCT  inda ya yi zargin cewa alakar shugaban kungiyar da jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ce ta yi tasiri wajen tafiyar da yajin aikin.

“Batun siyasa ne, don haka dole ne mu kawo karshen wannan dabi’a ta yin barazana ko matsin lamba. Mutumin da ya tsaya takara a zaben kananan hukumomi a karkashin jam’iyyar ADC shi ne shugaban NLC a FCT.

“Me kuke tsammanin zai yi? Tabbas zai yi kokarin ganin gwamnati ta gaza wajen gudanar da ayyukanta, domin ya yi amfani da hakan a matsayin yakin neman zabe cewa malamai suna yajin aiki,” in ji Wike.

Kalaman ministan sun biyo bayan damuwa game da batutuwan da ba a warware su ba tsakanin gwamnatin FCT da kungiyoyin kwadago  wadanda suka hada da zargin rashin biyan hakkokin malamai da kuma kudaden karin girma da ake bin su.

KARANTA KUMA: Yajin Aikin Malamai a FCT: Ministan FCT ya bayar da umarnin ‘Babu aiki, babu albashi’

Wike ya musanta zargin cewa gwamnatinsa na bin ma’aikata bashin albashi  inda ya yi nuni da irin saka hannun jari da aka yi wajen gyaran makarantun gwamnati da samar da muhimman ababen more rayuwa.

“Ba mu bin kowa bashi. Ku je ku ga makarantun a yau. Abin da muka yi a makarantun shi ne gyara su da kuma samar da muhimman ababen more rayuwa.

“Kungiyar kwadago Ba za Ta Iya Ci Gaba Da Yi Mana Barazana Ko matsin lamba ba,” in ji shi.

Da yake bayyana damuwarsa kan illar da yajin aikin ke haifarwa ga dalibai, ministan ya ce za a warware takaddamar, tare da yin gargadin cewa tsawaita yajin aikin na iya kawo cikas ga samun ilimi.

Ya kuma yi barazanar daukar matakin shari’a kan shugabannin kungiyar kwadagon inda ya bayyana cewa lauyoyin hukumar FCT na shirya shigar da kara a kotu.

“Dole ne a kawo karshen tattaunawar domin yara ne za su sha wahala a karshen lamarin amma kada ku damu za mu magance matsalar. Zan takaita karfin ikon shugaban NLC din,” in ji shi.

Dangane da sukar da ake yi masa kan yadda yake tafiyar da takaddamar Wike ya jaddada cewa duk wani mataki da hukumar FCT za ta dauka zai kasance ne bisa tsarin doka.

A ranar 7 ga watan Oktoba ne reshen kungiyar kwadago ta NLC a FCT ya ayyana yajin aiki na tsawon lokaci mara iyaka sakamakon rashin cimma matsaya kan takaddamar da ke tsakanin hukumar FCT da kungiyar malamai ta Najeriya (NUT).

Yajin aikin ya haifar da tsaiko ga harkokin karatu a makarantun gwamnatin da abin ya shafa lamarin da ya sanya dalibai cikin rashin tabbas game da lokacin da za a ci gaba da gudanar da darussa yadda ya kamata.

 

Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button