Siyasa

APC Da Kungiyar Arewa Sun Yi Kawance Don Kara Yawan Kuri’u A Zaben 2027

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi alkawarin yin aiki tare da kungiyar ‘Arewa for Asiwaju’ (A4A) domin tattara karin masu kada kuri’a a fadin yankin Arewacin Najeriya gabanin babban zaben shekarar 2027.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da shugabannin kungiyar A4A karkashin jagorancin tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Ibrahim Shekarau suka kai masa ziyara a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja.

KARANTA KUMA: APC ta nada Gwamnan Kwara a matsayin Mataimakin Shugaba

Farfesa Yilwatda ya bayyana cewa jam’iyyar za ta hada tsarin kungiyar cikin shirye-shiryen zabe domin karfafa yakin neman zabe da kuma inganta sakamakonta a zabukan shugaban kasa da Majalisar Dokoki ta Kasa gwamnoni da majalisun dokokin jihohi.

Ya yaba wa kungiyar bisa hada gwanayen shugabannin siyasa da matasa daga bangarori daban-daban inda ya bayyana tsarin kungiyar a matsayin mai hada kowa da kuma wakiltar yankin Arewacin Najeriya yadda ya kamata.

Shugaban na APC ya ce kungiyar za ta iya taimakawa wajen kawar da tunanin cewa gwamnatin Tinubu ta yi watsi da yankin Arewa ta hanyar bayyana ayyuka da shirye-shiryen da ake aiwatarwa a yankin.

Ya ambaci manyan ayyukan hanyoyi bututun iskar gas na Ajaokuta-Kaduna-Kano (AKK) da kuma damar samun rancen kudin karatu ga dalibai a matsayin misalan ayyukan da zai amfani al’ummar Arewa.

A cewarsa  ayyukan hanyoyi da ake ginawa ko kuma ake shirin fara ginawa a Arewacin Najeriya sun kai tsawon kilomita sama da 3,000.

Yilwatda ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki na yankin Arewa da su yi amfani da manufofi da shirye-shiryen gwamnati domin inganta ilimi da fadada damar samun ayyukan yi da bunkasa tattalin arziki da kuma tallafawa ci gaban yankin.

Ya ce jam’iyyar za ta yi aiki tare da A4A domin tattara goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu da ‘yan takarar APC a zaben 2027.

Tun da farko Sanata Shekarau ya bayyana cewa an kafa kungiyar A4A ne domin tattara masu kada kuri’a a jihohi 19 na Arewa da kuma Babban Birnin Tarayya (FCT).

Ya bayyana cewa kungiyar ta yi nazarin sakamakon zabukan da suka gabata domin gano wuraren da aka samu rauni karancin fitowar masu kada kuri’a, da kuma rashin sha’awar mutane wajen zabe inda ya kara da cewa za ta yi aiki don magance wadannan kalubale.

Sanata Shekarau ya ce wannan shiri zai taimaka wajen karfafa kokarin APC Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa da gwamnonin jihohi da sauran masu ruwa da tsaki a siyasa maimakon yin aiki daban daga tsarin jam’iyyar da ake da shi.
Ya kara da cewa kungiyar ta nada masu kula da harkokinta a jihohi da sauran matakai domin karfafa hadin kan jama’a a matakin tushe da kuma wayar da kan jama’a game da nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu a yankin Arewa.

Tsohon gwamnan ya kuma gayyaci Farfesa Yilwatda zuwa bikin kaddamar da sakatariyar kungiyar da aka tsara gudanarwa a ranar Asabar 17 ga Oktoba 2026 inda ya kara da cewa Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya amince da gayyatar.

Mataimakin Shugaban Kwamitin Amintattu na kungiyar wanda kuma tsohon Gwamnan Jihar Plateau ne Simon Lalong ya bayyana kungiyar ta A4A a matsayin dandamali da gogaggun shugabannin siyasa ke amfani da shi wajen tallafawa kokarin jam’iyyar APC a fagen zabe.

 

 

Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button