Kwallon Kafa Ta Bakin Teku: Alkalin Wasa Ya Yarda Da Kuskuren Da Ya Yi A Wasan Neman Gurbi Na Najeriya Da Ghana

Alƙalin wasa ɗan ƙasar Morocco Driss Lamghaidar da tawagarsa sun amince da kuskuren da suka yi na ba da damar ƙarin lokaci da bugun fenariti a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin ƙwallon ƙafa na bakin teku na Afirka (CAF Beach Soccer AFCON) na shekarar 2026 tsakanin Najeriya da Ghana a Kaduna ranar Asabar.
Manyan baƙi da masu kallo a filin wasan sun yi mamaki matuƙa lokacin da Lamghaidar da mataimakansa suka ba da umarnin a buga ƙarin lokaci sannan daga baya aka buga fenariti a wasan farko wanda ya ƙare da ci 3-3 a lokacin da aka tsara na wasan.
A wani taro da aka gudanar ranar Asabar da daddare Lamghaidar ya amince cewa ya yi kuskure wajen kai wasan zuwa ƙarin lokaci da kuma bugun fenariti kasancewar wasan farko ne kawai kuma ana sa ran buga wasa na biyu wanda zai tantance wanda zai yi nasara a ranar Lahadi 18 ga Oktoba a Keta Ghana.
Wannan yana nufin har yanzu sakamakon wasan bai tabbata ba kuma dukkan ƙungiyoyin biyu suna da damar yin nasara a wasan na biyu.
Isa Hamza Manga ya ci wa Najeriya ƙwallaye uku (hat-trick) yayin da Mawuli Sosu ya ci biyu Wise Nyamadi kuma ya ci ɗaya ga tawagar Black Sharks.
Sand Eagles sun sha kashi a hannun Ghana ta hanyar bugun fenariti a wasan neman gurbin shiga gasar BSAFCON
Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta ɗauki mataki nan take bayan wasan don neman ƙarin bayani game da batun ƙarin lokaci da bugun fenariti abin da ya saɓa wa ƙa’ida a wasan da ya ƙunshi karawa biyu kuma an buga na farko ne kawai.
Shugaban Hukumar Wasanni ta Ƙasa (NSC) Mallam Shehu Dikko Mukaddashin Babban Sakataren NFF Dr. Emmanuel Ikpeme Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Kaduna Ben Kure Mataimakan Musamman ga Shugaban NSC Musa Amadu da Clement Nwankpa Mukaddashin Mataimakin Babban Sakataren NFF Dr. Ademola Olajire da kuma Mataimakin Shugaban NSC na musamman Ahmad Muazu na cikin manyan jami’an NSC Gwamnatin Jihar Kaduna da NFF da suka kalli wasan a filin wasan ƙwallon ƙafa na bakin teku na Murtala Muhammed Square.



