Kipchoge Ya Samu Nasarar Gudun Maraton Ta Farko Cikin Shekaru Uku.

Eliud Kipchoge dan kasar Kenya kuma wanda ya taba lashe gasar Olympics sau biyu ya lashe gasar gudun Maraton ta Melbourne a ranar Lahadi tare da kafa sabon tarihin lokaci na sa’o’i 2 mintuna 9 da dakika 10 wannan shi ne karo na 17 da ya lashe gasar irin wannan yayin da yake da shekaru 41 a duniya.
Kipchoge na kokarin gudanar da gasar marathon a dukkan nahiyoyi bakwai cikin shekaru biyu bayan ya fara wannan shiri nasa na nahiyoyi a gasar Marathon ta Cape Town a watan Mayu.
Nasarar da ya samu a ranar Lahadi ita ce ta farko cikin shekaru uku bayan ya lashe gasar Berlin a shekarar 2023 inda ya kafa tarihin lashe gasar manyan ‘yan tseren duniya (majors) sau 11.
“Na yi imani cewa jikina har yanzu yana cikin yanayi mai kyau na fafatawa har yanzu ina iya yin gasa da sabon tsarar ‘yan wasa” cewar Kipchoge yayin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala tseren.
“Akwai tsoffin ‘yan wasa da ke ci gaba da fafatawa amma ina farin cikin yin gudu tare da matasan wannan zamani (Gen Z). Na kara saurin guduna bayan na kai kilomita 30 domin ganin ko zan iya yin gudu mai kyau har in karya tarihin lokacin tseren. Shirina ya yi nasara.”
Dan kasar Ostiraliya Thomas Do Canto ya zo na biyu bayan Kipchoge da lokacin 2:10:35 yayin da dan kasarsa Reece Edwards ya zo na uku da lokacin 2:14:33.
Camille French daga New Zealand ta lashe gasar mata da lokacin 2:28:25 sai Sinead Diver daga Australia a matsayi na biyu da lokacin 2:28:49 sannan Nichola Sheridan daga Ireland ta zo ta uku da lokacin 2:29:13.



