Shugaba Tinubu Ya Amince Da Karin Albashin Sojoji Da Ya Kai Kashi 80 Cikin Dari.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da a yi cikakken karin albashi ga ma’aikatan Rundunar Sojin Najeriya, inda karin zai kasance tsakanin kashi 30 zuwa 80 cikin dari, a matsayin wani bangare na kudirin gwamnatinsa na inganta jin dadin sojoji da karfafa tsaron kasa.
Ana sa ran kimanin sojoji 250,000 za su ci gajiyar wannan sabon tsarin albashi, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Satumba, kuma zai kara yawan kudaden da ake kashewa wajen biyan albashin sojoji a shekara daga Naira biliyan 660 zuwa Naira biliyan 924.
A cewar wata sanarwa daga Mai bai wa Shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru, Mista Bayo Onanuga, jami’an soji masu mukamin da ya zarce na ‘Colonel’ za su samu karin albashi na kashi 30 cikin dari.
Wannan karin ya shafi mukaman ‘Brigadier General’, ‘Major General’, ‘Lieutenant General’ da ‘General’, yayin da jami’an da ke da mukamin ‘Colonel‘ zuwa ‘Warrant Officer’ za su samu karin kashi 50 cikin dari. Sojoji daga mukamin ‘Private’ zuwa ‘Staff Sergeant’ kuma za su ci gajiyar karin albashi na kashi 80 cikin dari.
Shugaba Tinubu ya ci gaba da yaba wa jaruntaka, kwarewa da sadaukarwar da sojoji ke nunawa wajen tunkarar ta’addanci, ayyukan ‘yan fashi da garkuwa da mutane a fadin kasar nan.
“Dole ne a tallafa wa maza da matan da ke tabbatar da tsaronmu a gidajenmu tare da nuna musu godiya yayin da suke gudanar da ayyukansu ga kasarmu.
“Gwamnatarmu za ta ci gaba da ba da fifiko ga jin dadin sojoji da kuma zamantar da rundunar sojin ta hanyar samar da makamai da kayan aikin zamani da ake bukata wajen gudanar da ayyukansu.
“Gwamnatarmu ta yi imani cewa babu kasa da za ta iya samun daukaka ba tare da tsaro ba. Saboda haka, mun kuduri aniyar tattara dukkan karfin soji da na hukumomin tsaro domin kawar da barazanar tsaro da kuma kare rayuka da dukiyoyin dukkan ‘yan Najeriya.”
Shugaba Tinubu ya bukaci sojoji su dauki wannan karin albashi a matsayin alamar godiyar kasa mai zurfi kan kishin kasarsu, sadaukarwa da kuma hidimar da suke yi ba tare da gajiyawa ba.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa, ta hanyar ci gaba da jajircewarsu da kuma goyon bayan da gwamnati ke ci gaba da bayarwa, Najeriya za ta yi nasara kan dukkan karfin da ke barazana ga zaman lafiya, tsaro da hadin kan kasa.
Aisha.Yahaya, Lagos



