Shugaban NSDC Ya Umurci Ma’aikata Da Su Nuna Gaskiya Da Kuma Rikon Amana.

Babban Kwamandan Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC), Farfesa Ahmed Audi, ya yi kira ga ma’aikata da su nuna gaskiya da rikon amana wajen gudanar da ayyukansu domin cimma manufofin hukumar yadda ya kamata.
Wannan kira yana cikin sanarwar da Kakakin hukumar, Afolabi Babawale, ya fitar, inda ya bayyana cewa Babban Kwamandan ya yi wadannan kalamai ne a Abuja, yayin taron karbar sabbin jami’ai 100 na Sashen Yaki da Zamba (Anti-Fraud Unit) daga sassa daban-daban da kuma kaddamar da littattafai guda biyu da shugabar sashen ta rubuta.
Sanarwar ta bayyana cewa Farfesa Audi ya jaddada cewa ba za a iya gudanar da muhimman ayyukan hukumar na kare rayuka da dukiyoyi, tabbatar da zaman lafiyar jama’a, da inganta tsaron al’umma ba tare da gaskiya da rikon amana ba.
KARANTA KUMA: NSCDC ta Kaddamar da Yakin Wayar da Kan Jama’a kan Tsaron Kayan Aikin Sadarwa
“Zamba da cin hanci da rashawa barazana ce mai hadari da za ta iya lalata kokarinmu, rage amincewar jama’a a gare mu, da kuma raunana ginshikin hukumar tamu.
“Ba wai kawai suna shafar ayyukanmu ba ne, har ma suna bata sunan daukacin ma’aikatan gwamnati.
“A yau, muna daukar matakin yaki da wadannan barazanar, tare da jaddada kudurinmu na bin ka’idojin aiki da kuma nuna gaskiya da rikon amana,” in ji shi.
Domin nuna irin muhimmancin da hukumar ke baiwa ladabi da biyayya, Farfesa Audi ya bayyana cewa an sallami ma’aikata 37 daga aiki, yayin da wasu ke fuskantar shari’a saboda hannu cikin harkokin sayar da guraben aiki ta hanyar zamba, karbar cin hanci, safarar makamai, da sauran ayyukan da suka saba wa ka’idojin aiki.
A jawabinta na maraba, Shugabar Sashen Yaki da Zamba, Kwamanda Emeribe Chinyere Victory, ta bayyana cewa sashen ya ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da gaskiya, bayyana gaskiya, da rikon amana a daukacin hukumar, tare da cewa tun lokacin da aka kafa sashen a shekarar 2007 da kuma horon farko da aka yi a Cibiyar EFCC a 2008, shugabanni daban-daban sun ci gaba da inganta karfin ma’aikata.
Ta nuna godiyarta ga Farfesa Audi bisa samar da yanayi mai kyau na aiki ba tare da tsangwama ba, sannan ta kara da cewa sashen na ci gaba da gano, dakilewa, da kuma binciken ayyukan cin hanci da rashawa da suka shafi ma’aikata da ‘yan kwangila.
Taron ya kunshi kaddamar da littattafai guda biyu da Dr. Emeribe ta rubuta: *The Dark Side of Duty* da *The Anti-Fraud Lexicon*, wadanda Mataimakin Babban Kwamanda mai ritaya, Hammed Abodurin, ya yi sharhi a kansu.
An gabatar da sakonnin fatan alheri daga manyan masu ruwa da tsaki a fannin tsaro, ciki har da:
Hajiya Hafsat Abubakar Bakori, Shugabar Hukumar Kula da Bayanan Kudi ta Najeriya (NFIU); Peter Edako, wakilin Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA); DCP Adeola Odetunde, wakilin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP); da kuma ACG Lakitile Cyrus, wakilin Babban Kwanturola na Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali.
Aisha.Yahaya, Lagos



