Siyasa

Manoman Jihar Kwara Sun Goyi Bayan Shirin Shugaba Tinubu na Sake Tsayawa Takara

Manoma kimanin dubu 40,000 da suka yi rajista, tare da iyalansu a Jihar Kwara, sun bayyana goyon bayansu a hukumance ga sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kungiyar, wacce ke gudanar da ayyukanta a karkashin inuwar kungiyar manoma ta kasa (AFAN), ta kuma nuna goyon bayanta ga kudirin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na neman kujerar Sanata, da kuma kudirin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kwara, Yakubu Danladi-Salihu, na neman kujerar Gwamna.

An bayyana wannan goyon baya ne yayin wani taron manema labarai a Ilorin, babban birnin jihar, inda jami’an AFAN suka yi alkawarin tattara manoma da iyalansu a fadin kasar domin tabbatar da nasarar dukkan ‘yan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a fadin jihar.

KARANTA KUMA: INEC ta yi wa masu ruwa da tsaki bayani kan shirye-shiryen zaben 2027

Yayin da yake zantawa da manema labarai tare da sauran shugabannin kungiyar Shugaban AFAN na jiha Malam Shuaib Ajibola, da mai gudanarwa, Alhaji AbdulRahman Babatunde, sun bayyana cewa goyon bayan da suka bayar ya samo asali ne daga tasirin sauye-sauyen da manufofin Gwamna AbdulRazaq a fannin noma da shirye-shiryen tallafi masu dorewa suka haifar.

Da take bayyana manyan nasarorin da gwamnatin jihar ta samu, kungiyar ta yi nuni da wasu muhimman matakan tallafi na kudade da kayan aikin noma, kamar bayar da rancen tallafi na Naira biliyan 2 ga manoman da annobar COVID-19 ta shafa, raba tallafin masara ga mutane sama da dubu 10,000, da kuma ci gaba da bayar da tallafin rage farashin muhimman kayan aikin noma kamar iri masu ba da amfani mai yawa, iri masu jure fari, magungunan kashe ciyawa, da takin zamani.

Bugu da kari, shugabancin kungiyar ya yaba wa gwamnatin jihar bisa daukar nauyin Baje-kolin Noma na 7 a shekarar 2024 da kuma raba kayan aikin noma (masara) ga wasu karin manoma 2,000 a kwanan nan.

Sun kuma yaba da yadda jihar ke taka rawar gani a shirye-shiryen ci gaba kamar su Livestock Productivity and Resilience Support Project (L-PRESS) Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (ACReSAL) Special Agro-Industrial Processing Zones (SAPZ), da kuma shirin FADAMA; wadanda dukansu suka taimaka matuka wajen bunkasa yawan amfanin gona da inganta rayuwar al’umma a yankunan.

Sakamakon haka, kungiyar ta sake jaddada kudirinta na gudanar da ayyukan tattara goyon bayan jama’a a dukkan al’ummomin manoma na karkara domin tabbatar da nasara mai karfi ga jam’iyyar APC a zaben shekarar 2027

 

 

Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button