Najeriya

NSCIA Ta Fadada Majalisar Zartarwa Ta Kasa

Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta sake fasali tare da fadada Majalisarta ta Zartarwa ta Kasa (NEC).

A cewar sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na NSCIA Abbas Jimoh ya sanya wa hannu an cimma wannan matakin ne a yayin Babban Taron Majalisar da aka gudanar a ranar 1 ga Oktoba 2026 a Abuja babban birnin tarayyar kasar.

Mista Jimoh ya bayyana cewa bisa sabon tsarin an nada Farfesa Mahfouz Adedimeji a matsayin Mataimakin Babban Sakatare na Kasa yayin da Farfesa Salisu Shehu zai rike mukamin Mataimakin Babban Sakatare na Harkokin Kasashen Waje (na Duniya). Mista Abeny Mohammed (SAN) ya zama Mataimakin Babban Sakatare na Harkokin Kamfanoni da Kungiyoyi shi kuma Dr. Bala Muhammad ya zama Mataimakin Babban Sakatare na Harkokin Gudanarwa.

An nada Dr. Umar Jibrilu Gwandu a matsayin Jami’in Hulda da Jama’a tare da Hajiya Sekinat Lawal a matsayin Mataimakiyarsa. Sauran wadanda aka nada sun hada da Dr. Mairo Mandara Jami’ar Harkokin Ci Gaba Architect Abdullahi Musa PenAbdul Mataimakin Jami’in Harkokin Ci Gaba (bangaren Fasaha) da kuma Farfesa Fatimah Abdulkarim Jami’ar Harkokin Iyali.

Ya ce taron ya samu halartar shugabannin Musulmi sarakunan gargajiya da manyan limamai daga jihohi 36 da kuma Babban Birnin Tarayya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button