Jam’iyyar APC Ta Yankin Arewa Ta Tsakiya Ta Gudanar Da Babban Taro A Lafia.

Jam’iyyar APC ta yankin Arewa ta Tsakiya ta shirya wani babban taron gangami a Lafia babban birnin jihar Nasarawa a ranar Asabar mai zuwa.
Wata sanarwa da Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC Dele Alake ya sanya wa hannu a ranar Asabar ta bayyana cewa taron na daga cikin shirin kungiyar tattara goyon bayan jama’a ta yankin (Grassroots Mobilisation Movement) domin goyon bayan sake zaben Shugaba Tinubu da Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima a shekarar 2027.
A yayin taron kaddamar da kungiyar wanda aka gudanar a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) da ke Abuja a ranar Juma’a Sanata George Akume ya yaba wa shugaban kungiyar na kasa Mista Sonny S.T. Echono bisa nasarar kafa kungiyar inda ya jaddada cewa yankin Arewa ta Tsakiya yana da babban burin samar da mafi yawan kuri’u ga Shugaba Tinubu a yankunan kasar.
KARANTA KUMA: APC Ta Jihar Akwa Ibom Ta Fara Shirye-Shiryen Tarukan Zaben Shugabannin Jam’iyya Na 2026
Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule shi ma ya yaba da wannan mataki tare da bayyana cewa kalubalen da ke tattare da zaben 2027 na raguwa a hankali inda ya ce sabon rajistar masu zabe ya nuna akwai karfin goyon baya ga jam’iyyar APC a yankin Arewa ta Tsakiya.
Ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa yankin zai samar da mafi yawan kuri’u ga Shugaban Kasa da sauran ‘yan takarar da ke neman mukamai a karkashin jam’iyyar APC.
Ya yi nuni da cewa karfin siyasar yankin Arewa ta Tsakiya wanda a halin yanzu yake da Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) Shugaban jam’iyyar APC na kasa da kuma wasu muhimman jami’an gwamnati da aka nada ya fi karfin da yake da shi a baya kafin zaben da ya gabata sosai.
Ya bayyana cewa yankin zai yi amfani da kungiyar ‘North Central Grassroots Mobilisation Movement for Tinubu/Shettima wajen kai sakon jam’iyyar zuwa matakin tushe da kuma tattara goyon baya a fadin yankin.
Mista Echono ya ce batun yanzu ya wuce kawai ko Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu nasara a yankin Arewa ta Tsakiya a’a batun ya shafi yadda yankin zai tsara kansa domin samar da mafi yawan kuri’u ga Shugaban kasa a zaben shekarar 2027.
Echono ya yaba wa Sakataren Gwamnatin Tarayya Sanata George Akume da Kungiyar Gwamnonin Arewa ta Tsakiya da sauran masu ruwa da tsaki a yankin bisa jajircewarsu da goyon bayan da suke bai wa gwamnatin ‘Renewed Hope’ (Sabon Fata) ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ya ce kungiyar za ta zama muhimmiyar kafa ta fara ayyuka da kuma dandalin tattara goyon baya bisa tsari inda za ta hada shugabannin siyasa masu fafutuka a matakin tushe da sauran masu ruwa da tsaki na yankin Arewa ta Tsakiya domin cimma manufa daya gabanin zaben 2027.
Ministan Yada Labarai Alhaji Mohammed Idris Malagi ya bayyana wannan kungiya a matsayin ta irinta farko.
A karshen taron kungiyar ta cimma matsaya kan kara kaimi wajen tattara goyon bayan Shugaba Tinubu domin zaben 2027 da nufin samar da mafi yawan kuri’u daga yankin.
Haka kuma an amince a shirya shirin bayar da tallafin kiwon lafiya da kafa kwamitin sulhu da kuma shirya tarukan tattaunawa da jama’a a fadin yankin.
Kungiyar ta yanke shawarar cewa Ministan Yada Labarai zai yi aiki tare da Kwamishinonin Yada Labarai na jihohi da Sakatarorin Yada Labarai na jam’iyya a jihohi da kuma kwamitocin yada labarai na jihohi domin fadakar da jama’a game da wannan shiri tare da goyon bayan gwamnonin jihohin.



