Najeriya

Shugaban Kasa Tinubu Ya Taya Janar Akinrinade Murnar cika shekaru 87

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Babban Hafsan Sojojin Kasa kuma dattijo mai kishin kasa Janar Alani Ipoola Akinrinade (mai ritaya) murnar cika shekaru 87 da haihuwa inda ya bayyana shi a matsayin gwarzon soja kuma dan kasa mai kishin kasarsa da tsayawa kan ka’ida wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa Najeriya hidima.

A cikin sakon taya murna da mai magana da yawun Shugaban kasa Mista Bayo Onanuga ya sanya wa hannu Shugaba Tinubu ya yaba wa Janar Akinrinade bisa ci gaba da yi wa kasa hidima a matsayin dattijo mai kishin kasa da kuma gudummawar da ya bayar wajen hadin kan kasa.

Shugaban ya bayyana Janar din mai ritaya a matsayin “mai ba da shawara mai cike da hikima da daidaito” tare da nuna muhimmancin rawar da ya taka wajen ci gaban dimokuradiyyar Najeriya.

KARANTA KUMA: Oyetola Ya Taya Dattijo Mai Kishin Kasa Akinrinade Murnar Zagayowar Ranar Haihuwarsa

“Janar Akinrinade ya tsaya a gefen da ya dace a tarihin kasa. A lokacin da yin hakan ke da hadari ya zabi dimokuradiyya maimakon mulkin kama-karya ya kuma zabi jama’a maimakon iko.

“Yana daya daga cikin jaruman da suka ba da damar samar da Jamhuriya ta Hudu. Najeriya za ta ci gaba da godiya gare shi bisa jajircewarsa da sadaukarwarsa” cewar Shugaba Tinubu.

Ya ce tarihin ayyukan Janar Akinrinade ya kafu sosai a tarihin Najeriya tun daga fitaccen aikinsa na soja wanda ya kai ga jagorantar Rundunar Sojojin Najeriya har zuwa rawar da ya taka a matsayin jagoran kungiyar National Democratic Coalition (NADECO) yayin gwagwarmayar da aka yi don maido da sakamakon zaben 12 ga watan Yuni da kuma dimokuradiyya.

Shugaban ya kuma yaba wa tsohon shugaban sojojin bisa ci gaba da nuna jajircewa wajen ci gaba da hadin kan kasa.

“A madadin Gwamnati da al’ummar Najeriya Shugaban kasa yana yi wa Janar Akinrinade addu’ar samun cikakkiyar lafiya kwanciyar hankali da kuma karin shekaru masu yawa na rayuwa mai amfani” in ji shi.

Shugaba Tinubu ya yi wa dattijon mai kishin kasa fatan samun bikin cika shekaru 87 mai cike da farin ciki da gamsuwa.

A matsayinsa na tsohon soja da ya yi yakin basasar Najeriya Janar Akinrinade ya rike mukamin Babban Hafsan Sojojin Kasa sannan daga baya ya zama Babban Hafsan Tsaron Kasa kafin ya yi ritaya daga aikin soja.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button